INEC Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

INEC Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Atiku Ya Fadi Zaben Shugaban Kasa

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gayawa kotu dalilin da ya sanya Atiku bai cancanci lashe zaɓen shugaban ƙasa ba
  • INEC ta ce ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP bai cika ƙa'idojin sa za su sanya a bayyana shi wanda ya lashe zaɓen ba
  • Hukumar INEC ta kuma gayawa kotun cewa Tinubu halastaccen ɗan takarar da yayi nasara a zaɓen

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, bai cika sharuɗɗan da za a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa ba.

Jaridar Channels Tv ta rahoto cewa INEC ta buƙaci kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa da tayi watsi da ƙarar da Atiku da jam'iyyar sa ta PDP suka shigar.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Magana Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya APC Ta Kasa Karbar Mulki a Hannun PDP a Wata Babbar Jiha

Atiku bai cika sharuddan lashe zabe ba
Dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar Hoto: The nation.com
Asali: UGC

Hukumar ta bayyana cewa ɗan takarar ya kasa samun akalla kaso ɗaya bisa hudu na ƙuri'un da aka kaɗa a cikin aƙalla biyu bisa uku na jihohin ƙasar nan da birnin tarayya Abuja, a dalilin hakan ba zai bayyana shi matsayin wanda ya lashe zaɓen ba.

The Nation tace sɓanin iƙirarin da masu shigar da ƙarar suke yi, INEC ta ƙara da cewa an gudanar da zaɓen ne cikin bin umurnin sabuwar dokar zaɓe ta 2022, sannan zaɓen cike yake da sahihanci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar INEC ta ce zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, shine sahihin wanda ya lashe zaɓen.

A zaɓen shugaban ƙasar, Tinubu ya ƙuri'u 8,794,726 inda yayi nasara akan Atiku wanda ya samu ƙuri'u 6,984,520 da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party wanda ya samu ƙuri'u 6,101,533. Atiku da Tinubu kowanen su ya ci ci zaɓe a jihohi 12, yayin da Obi ya lashe jihohi 11

Kara karanta wannan

Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android, Ya Kone Kurmus

Atiku da Obi sun garzaya kotu domin ƙalubalantar bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar INEC tayi.

Hukumar ta bayyana cewa ɗan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya cika dukkanin sharuɗɗan da doka da suka cancanci su sanya a bayyana shi a matsayin wanda yayi nasara.

APC Ta Kawowa Kotu Hujjar da Za Ta Iya Ruguza Takarar Peter Obi

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta gabatar da wata hujja a gaban kotu wacce zata iya ragargaza takarar Peter Obi.

Jam'iyyar APC ta dai gabatar da hujjar ne yayin da ta ke mayar da martani kan ƙarar da Peter Obi ya shigar yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng