INEC Ta Fitar Da Sabbin Bayanai Kan Zaben Cike Gurbi Na Jihar Rivers
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen cike gurbina jihar Rivers, ranar Asabar mai zuwa
- Zaɓen a cewar INEC za a gudanar da shi ne a rumfunan zaɓe 377 a cikin mazaɓu uku da cikin birnin Port Harcourt
- A cewar INEC yana da kyau dukkanin masu rajistar katin zaɓe a inda za ayi zaɓen su fito su kaɗa ƙuri'un su
Jihar Rivers - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Rivers ta sanar da cewa za a gudanar da zaɓen cike gurbi a kujerun majalisar wakilai ta tarayya na Port Harcourt II da Khana/Gokana, a ranar Asabar, 15 ga watan Afirilun 2023.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa kwamishinan zaɓen INEC na jihar Rivers, Johnson Sinikiem, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata 11 ga watan Afirilu, inda ya ce za a gudanar da zaɓen a ranar 15 ga watan Afirilun 2023.
Kwamishinan ya bayyana cewa za a fara gudanar da zaɓen ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a cikin ƙananan hukumomin da abin ya shafa.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Rivers ta sanar da jam'iyyu da sauran mutane cewa zaɓen cike gurbi na kujerun majalisar wakilan tarayya na Port Harcourt II da Khana/Gokana, zai gudana a ranar 15 ga watan Afirilun 2023 da misalin ƙarfe 8:30 a rumfunan zaɓen da abin ya shafa."
"Hukumar tana kuma kira ga masu rajistar katin zaɓe a mazaɓun da abin ya shafa da su fito kwansu da kwarkwatar su a ranar zaɓen domin kaɗa ƙuri'un su cikin kwanciyar hankali."
“Muna tabbatar muku da cewa a shirye mu ke domin ganin zaɓukan sun kammalu cikin nasara."
Dalilin Da Ya Sanya APC Ta Kasa Karbar Mulki a Hannun PDP a Wata Babbar Jiha
A wani labarin na daban kuma, an bayyana dalilin da ya sanya jam'iyyar APC ta kasa karɓe mulki a hannun jam'iyyar PDP a jihar Oyo.
Wata ƙungiyar magoya bayan Tinubu itace ta bayyana dalilan da suka sanya jam'iyyar kasa amsar mulki a hannun Gwamna Seyi Makinde.
Asali: Legit.ng