Gwamna Wike Ya Goyi Bayan Zanga-Zangar PDP, Ya Ce Bai Aminta da INEC Ba

Gwamna Wike Ya Goyi Bayan Zanga-Zangar PDP, Ya Ce Bai Aminta da INEC Ba

  • Gwamna Nyesom Wike ya goyi bayan matakin da jam'iyyar PDP ta ɗauka a jihar Ribas bayan kammala babban zaɓen 2023
  • Mambobin PDP sun tsunduma zanga-zanga a ofishin INEC na jihar tsawon mako biyu kenan suna neman a basu kayayyakin zaɓe su duba
  • Hakan na zuwa ne bayan jam'iyyun adawa sun kalubalanci zaɓen jihar a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya goyi bayan zanga-zangar da mambobin PDP ke gudanarwa yanzu haka a hedkwatar hukumar zaɓe (INEC) ta jihar, Premium Times ta rahoto

Zanga-zangar da 'ya'yan PDP su ke gudanarwa a hedkwatar INEC da ke gefen babban Titin Aba/Patakwal ta shiga mako na biyu kenan, sun buƙaci a basu kayan babban zaɓen 2023 su duba.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Gwamnan jihar Ribas na jam'iyyar PDP, Nyesom Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Da yake jawabi ga 'yan jarida ranar Talata, Wike ya yi karin haske kan zanga-zangar da cewa suna haka ne don zama cikin shiri domin sun san abinda 'yan adawa zasu iya aikatawa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP Ta Watsar da Gwamnoni 5, Ta Naɗa Wani Gwamna da Jigo a Babban Muƙami

Wike ya ce jam'iyyar PDP na bukatar INEC ta damƙa mata asalin sahihan takardun sakamakon zaɓe domin kare kanta a shari'ar da ake tafkawa a Kotun sauraron kararrakin zaɓe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A rahoton Channels tv, Gwamnan ya ce:

"Muna ankare da komai, duk wasu kulle-kulle, dukkan sakamakon da suka bugo zasu gabatar a gaban Kotun zaɓe muna da su a cikin kundin Flash," Wike ya faɗa yana ɗaga shi kowa ya gani.

"Saboda idan ka ce meke faruwa a Patakwal? Babu komai, kawai muna bukatar zama a cikin shiri ne. Bamu yarda da INEC ba kuma bamu aminta da 'yan sanda ba."
"Don haka muka ƙara kula sosai, ba mu fatan abinda ya faru a shekarar 2015/2016 ya sake faruwa da mu a karo na biyu."

Bugu da ƙari, gwamnan ya ce INEC ba ta da matsala a matsayinta na hukuma mai zaman kanta amma wasu mutane da ke aiki a hukumar ne, "Matsiyata."

Kara karanta wannan

"Mu Tari 2027" Sanatan APC Ya Yi Magana Kan Sahihancin Zaben 2023, Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi

Gwamna Wike Ya Ƙara Yi Wa Ayu Shagube

A wani labarin kuma Gwamnan Ribas ya sake taɓo tsohon shugaban PDP, ya ce ba abinda zai iya tsinanawa jam'iyyar a zaɓe

Wike, jagoran G-5, ya nuna jin daɗinsa da cewa gara da Allah ya sa Ayu bai yi murabus tun farko ba domin da wasu sun samu wurin ɗora alhakin rashin nasarar Atiku.

Gwamnan na ɗaya daga cikin fusatattun gwamnonin PDP 5 da suka ware, suka nemi Ayu ya yi murabus daga shugabancin jam'iyya amma ya ƙeƙashe ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262