'Yan Kwamiti Sun Fusata Sun Dakatar Da Shugaban Jam'iyyar APC

'Yan Kwamiti Sun Fusata Sun Dakatar Da Shugaban Jam'iyyar APC

  • Rashin gamsuwa da kamun ludayin shugabancin sa, ya sanya an dakatar da wani shugaban APC a jihar Ondo
  • An dakatar ne dai da shugaban jam'iyyar APC ɗin ne na mazaɓar Isaipen 8 a ƙaramar hukumar Owo ta jihar
  • Ƴan kwamitin zartarwar jam'iyyar ne dai a mazaɓar suka yanke wannan hukuncin inda suka lissafo dalilan su

Jihar Ondo- Kwamitin zartarwa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a mazaɓar Isaipen 8 a Owo, cikin ƙaramar hukumar Owo ta jihar Ondo, ya dakatar da shugaban jam'iyyar na mazaɓar, Mr. Olayode Omorayewa, bisa zargin rikon sakainar kashi da aikin sa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa dakatarwar tasa tana ƙunshe ne a cikin wata takarda da mambobin kwamitin 24 na mazaɓar suka rattaɓawa hannu, sannan suka aikewa da shugaban jam'iyyar na ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Bayan Dogon Lokaci, Gaskiyar Abinda Ya Sa Atiku Ya Sha Kaye a Zaben 2023 Ya Fito

An dakatar da wani shugaban APC
Wajen wani kamfen din jam'iyyar APC Hoto: Punch
Asali: UGC

Dakatarwar da aka yi wa Omarayewa, zata fara aiki ne tun daga ranar 9 ga watan Afirilun 2023, cewar rahoton The Hope Newspaper

Shugabannin sun nuna rashin ƙwarin guiwar su kan Omorayewa, kan yadda ya kasa ciyar da jam'iyyar gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun kuma yi ƙorafin cewa shugaban a yadda yake gudanar da shugabancin jam'iyyar, ba zata samu wani tagomashi ba na a zo a gani.

Daga cikin dalilan da suka bayar a cikin takardar dakatar da shugaban, har da tsatstsamar dangantakar da ke a tsakanin sa da sauran shugabannin jam'iyyar na mazaɓar.

Wani ɓangare na takardar na cewa:

“Bayan tattauna sosai da shawarwari, mun amince gabaɗaya cewa shugaban jami'iyyar na mazaɓar mu, baya samar da ingantaccen shugabancin da ake buƙata, sannan halayyar sa tana kawo rarrabuwar kai a tsakanin ƴaƴan jam'iyya."
"Dole ne a sake duba kan yiwuwar cigaba da zaman sa a matsayin shugaban jam'iyyar na mazaɓar domin duba mafitar jam'iyya."

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Ce Jam'iyyar Ta Cancanci Kayen Da Ta Sha a Zabe, Ya Bayar Da Dalilai

PDP Ta Watsar Da 'Yan G5 Ta Naɗa Adeleke a Babban Muƙami

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar PDP ta watsawa su Wike da Makinde, ta jingine su dangane da gudanar da zaben fidda gwanin gwamnan jihar Bayelsa.

Gwamna Wike da ƴan tawagar sa ta G5 sun daɗe suna takun saƙa da shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng