Abu 1 da Ya Taimaki Bola Tinubu Ya Iya Lashe Zaben Shugaban Kasa Inji Farfesa Sagay

Abu 1 da Ya Taimaki Bola Tinubu Ya Iya Lashe Zaben Shugaban Kasa Inji Farfesa Sagay

  • Itse Sagay SAN ya ce Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zabe ne domin ya fi kowa yin tanadi gabanin zaben
  • Farfesan yana ganin a cikin masu neman mulki, ‘Dan takaran APC ya fi shiryawa zaben 2023
  • Sagay ya yi kira ga magoya bayan Jam’iyyar LP su sallamawa kotu, su koma su yi shiri da kyau

Abuja - Shugaban kwamitin shugaban Najeriya kan yaki da rashawa na PACAC, Farfesa Itse Sagay ya yi bayanin abin da ya taimakawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben bana.

A ranar Lahadi, The Nation ta rahoto Farfesa Itse Sagay yana mai cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana da tsari mai kyau, kuma ya shiryawa takara.

Lauyan ya yi watsi da zargin da ake yi na magudi, yake cewa an yi zaben gaskiya a Fubrairu.

Kara karanta wannan

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

Farfesa Sagay ya yi fatali da hasashen da wasu suka rika yi na cewa Peter Obi na jam’iyyar LP yana gaban sauran ‘yan takarar kujerar shugabancin kasa.

Bola Tinubu ya shirya da kyau

Dattijon yake cewa bai yi mamaki da sakamakon zaben bana ba domin Bola Tinubu ya yi tanadi da kintsi fiye da na sauran abokan gwabzawarsa a zaben.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Sagay, na’urar BVAS da hukumar INEC ta kawo ta yi aiki sosai, a game da wadanda suka sha kashi, Farfesan ya ba su shawara su saurari kotu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu wajen kamfe Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An nemi masu ta-cewa su tafi kotu

Kamar yadda Farfesa Wole Soyinka ya fada, da aka yi hira da shugaban PACAC a tashar Channels, ya nuna a bar Alkalai su yi aiki ba tare da barazana ba.

Ko da ba suyi nasara a kotun zabe ba, kwararren Lauyan ya yi kira ga ‘yan siyasa su tari gaba, yake cewa su shiryawa zaben da za ayi nan da shekaru hudu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Abun da Ya Kamata Atiku, Peter Obi da Sauransu Su Yi

"Zan bada shawara ga wadanda suka fadi, musamman 'Yan jam’iyyar LP da su koma mazabu, su fara shiryawa, ba su da wani tsari.
Idan ku ka duba zabukan Gwamnonin jihohi, zai tabbatar da cewa jam’iyyar LP ba ta da wani tushe a kasar nan, wata guguwa ce kurum.
Abin da ya taimaki Tinubu ya yi nasara shi ne, duk inda bai zo na farko ba, shi ne na biyu a baya. Ba a taba zaben da ya fi wannan kyau ba.
Tinubu ne na farko a Kudu maso Yamma, na farko a Arewa maso Tsakiya. Duba kuri’un Arewa, a Kudu maso Gabas ne kawai bai ci kuri’u ba."

- Itse Sagay

APP ta ce akwai magudi a 2023

A rahotonmu, an ji Lauyan jam’iyyar APP a kotun karar zabe ya ce APC tayi magudi a Kano, Kaduna, Kebbi, Ribas, Oyo, Ogun, Ekiti, Kogi da Kwara.

Jam’iyyun da suka yi karar Bola Tinubu a kan zargin magudin zabe sun kara yawa zuwa biyar, APP ta je kotu duk da kuri’u 12, 000 ta samu a 2023.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng