An Lissafa Biliyoyin Kudin da ‘Yan Majalisa 1,200 Za Su Samu Daga 2023 Zuwa 2027
- Albashi da alawus na duka ‘Yan majalisar Najeriya a tsawon shekaru hudu yana neman kai N50bn
- Nan da 2027, ‘Yan majalisar wakilai da Sanatocin tarayya za su raba Naira biliyan 32 tsakaninsu
- ‘Yan majalisar dokoki da ke jihohi 36 za su kashe Naira biliyan 16.32 da sunan alawus da albashi
Abuja - An fadi albashi da jerin alawus da za a rika biyan ‘yan majalisar Najeriya a matakin jihohi da na tarayya na tsawon shekaru hudu da za su yi a ofis.
Punch ta ce wadannan mutane da adadinsu bai wuce 1,253 ba, za su tashi da kusan Naira biliyan 49 daga cikin baitul-mali kafin wa’adinsu ya kare.
An tattara kudin da za a biya ne daga bayanan da ke kan shafin hukumar RMAFC mai alhakin yanka albashin ‘yan siyasa da ma’aikatan Najeriya.
Amma ana tunanin hakikanin abin da ‘yan majalisar ke samu, ya fi karfin abin da ake sanarwa.
N16bn a Jihohi, N32bn a Abuja
A matakin tarayya, ‘Yan majalisar wakilai da Sanatoci za su samu Naira biliyan 32.60. A majalisar dokoki na kasa, za a batar da Naira biliyan 16.32.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Idan aka bi abin dalla-dalla, rahoton ya ce albashin shugaban majalisar dattawa a duk wata ya kai N2.48m (a shekaru hudu zai samu kimanin N9.94m.)
Ruwan albashi da alawus
A duk wata, ana biyan N2.31m ga Mataimakin shugaban majalisar, wanda a shekaru hudu zai karbi N9.24m, wannan ba a maganar alawus iri-iri.
Shi kuwa shugaban majalisar wakilai yana da albashin N2.48m a wata (N9.91m a shekaru hudu), mataimakinsa zai bar ofis da N91.5m a albashi kurum.
Alawus din shugaban majalisar wakilai ya kai akalla N18.33m, sai mataimakinsa zai samu N17.16m domin kula da mazaba, shakatawa da sauransu.
Shugabannin majalisun dokoki su na karbar N6.56m a shekara hudu, sai mataimakansu su samu N5.8m. Idan aka tattara alawus, ana maganar N1.5bn.
Sauran ‘yan majalisar wakilai su na da N1.9m da sunan albashi a shekara, N7.94m a shekaru hudu, sai alawus da akalla ya kai N58.76m kafin su sauka.
Daukacin ‘yan majalisar za su ci N2.8bn a albashi da wasu N21.04bn a alawus. A jihohi kuwa, mutum 784 za su raba N14.36bn nan da Mayun 2027.
Takarar Hon. Yusuf Gagdi
An samu labari wani ‘Dan Majalisar APC da ya fito neman shugabancin majalisa, yana yin kamfensa a asirce, ba kowa ba ne shi illa Yusuf Gagdi.
‘Dan majalisar na shiyyar Pankshin, Kanke da Kanam ya sha alwashin cewa zai kawo karshen cuwa-cuwar kasafin kudi idan ya samu shugabanci.
Asali: Legit.ng