Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

  • Sanatocin APC da-dama sun dage wajen harin zama Shugaban majalisar dattawa a Najeriya
  • A majalisar wakilan tarayya, masu kamfe sun yin isa wajen gaje kujerar Femi Gbajabiamila
  • Da alama halin da aka shiga zai iya jawo Bola Tinubu da ya bar kasar, ya dawo a makon gobe

Abuja - A yayin da neman shugabancin majalisar wakilai da dattawa ya kara daukar zafi, ‘yan APC sun fara daukar mataki domin gudun a samu matsala.

Kamar yadda rahoto ya fito a Punch a ranar Lahadi, zuwa farkon mako mai zuwa ake sa ran Bola Tinubu zai katse abin da yake yi a kasar waje, ya dawo.

Idan hakan ta tabbata, ranar Litinin dinnan zababben shugaban na Najeriya zai bar duk wasu abubuwan da yake yi a ketare, ya tattara ya shigo kasar.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Jam'iyyar APC ta kori wani fitaccen sanata a jihar Arewa

Ana tunanin Bola Tinubu zai dawo Najeriya domin ya shawo kan al’amuran jam’iyyar APC da suka shafi takarar shugabancin 'yan majalisar da za a rantsar.

Halin da ake ciki a yau

Zuwa yanzu APC ta na da kujeru 57 a majalisar dattawa, LP ta na takwas, NNPP da SDP su na da biyu, sai aka samu mutum daya da ya ci zabe a YPP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan Benuwai ta Kudu, Abba Moro ya ce babu wata doka da ta ce sai daga jam’iyya mai rinjaye za a samu shugaban majalisa, amma hakan ya zama al’ada.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a jirgin sama Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

A jihohin Kebbi, Zamfara da Sokoto, ba a karasa zaben majalisar tarayya ba. Amma bisa dukkan alamu jam’iyyun APC da PDP ne za su raba kujerun yankin.

A hasashenmu, APC za ta iya samun karin kujeru uku ko hudu, yayin da Sanatocin PDP za ta karu da biyar bayan INEC ta karasa zabuka a mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

An Samu Wanda Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa, Ya Ziyarci Gwamnoni 24 a Boye

Sanatoci da 'Yan majalisa sun shirya

Sanatocin da ke neman shugabanci sun hada da Jibrin Barau, Sani Musa, Orji Kalu, Godswill Akpabio, Osita Izunaso, Peter Ndubuze da kuma Abdul’Aziz Yari.

Jam’iyyar APC ba ta fito ta ware yankin da za su nemi kujerun shugabanni kamar yadda aka saba yi a baya ba, hakan ya bude kofa masu takarar suka yi yawa.

A gefe guda, rahoton ya ce masu hangen kujerar Femi Gbajabiamila su na bin duk hanyoyin da za su iya wajen ganin sun kai ga nasara nan da wasu kwanaki.

Hon. Gagdi ya ziyarci Gwamnoni 24

Wani ‘Dan Majalisar APC da ya fito neman shugabancin majalisa, yana yin kamfensa a asirce, rahotonmu ya tabbatar da ba kowa ba ne wannan illa Yusuf Gagdi.

‘Dan majalisar na shiyyar Pankshin, Kanke da Kanam ya ziyarci Gwamnoni 24 da Gwamna mai-jiran gado a Abia da kuma wasu masu fada a ji a karkashin LP.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zolayi Gwamnoni Da Suka Sha Kaye A Zaben Sanata, Ya Aika Sako Ga Yan Siyasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng