“Kada Ku Yi Murna Tukuna”: Primate Ayodele Ya Ce Ana Iya Tsige Uba Sani Da Wasu 3
- Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya yi gargadin cewa ana iya tsige zababbun gwamnonin Kaduna, Enugu da Ogun
- Malamin addinin ya ambaci sunayen wasu yan takara daga PDP da Labour Party da ka iya kalubalantar sakamakon zaben a kotu kuma su yi nasara
- Fasto Ayodele ya kuma yi hasashe game da zaben cike gurbi da za a yi a jihar Adamawa
Lagos - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe game da yiwuwar tsige zababbun gwamnonin wasu jihohi da maye gurbinsu da yan takarar jam'iyyun adawa.
A cewar wata sanarwa daga kakinsa, Osho Oluwatosin, Primate Ayodele ya bayyana cewa dan takarar PDP a jihar Kaduna, Isah Ashiru na iya yin nasara a kotu kuma hakan ya kai ga tsige Uba Sani na APC, jaridar Daily Independent ta rahoto.
A jihar Enugu, Primate Ayodele ya ba da shawarar cewa kada dan takarar PDP, Peter Mbah, ya yi murna tukuna domin jam'iyyar Labour Party na iya zama ainahin wacce ta lashe zaben a kotu.
"Kada zababbun gwamnonin jihohin Kaduna da Enugu su yi murna tukuna," Ayodele ya yi gargadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dalilin da ka iya sa a tsige Gwamna Dapo Abiodun - Primate Ayodele
Primate Ayodele ya kuma bayyana cewa babu tabbass a kan kujerar Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, kuma PDP na da damar kalubalantarsa a kotu koda dai ya bukaci jam'iyyar da ta sake dabaru don nasara.
Malamin ya kuma ba dan takarar gwamnan Labour Party a jihar Lagas, Gbadebo Rhodes-Vivour, shawara da kada ya shigar da kara kotu domin zai zama asarar kudi, kamar dan takarar gwamnan jihar Abia.
Zaben gwamnan Adamawa na 2023
A halin da ake ciki, Primate Ayodele ya kuma yi hasashe game da zaben cike gurbi a jihar Adamawa, yana mai cewa ba lallai ne yar takarar APC, Aishatu Binani ta yi nasara ba.
Sai dai kuma, ya gargadi dan takarar PDP, Ahmadu Fintiri, da ya zama a ankare domin ya hango magudi daga bangaren APC, Nigerian Tribune ta rahoto.
Gwamnatin wucin gadi: Primate Ayodele ya yi sabon hasashe gabannin rantsar da Tinubu
A wani labarin, Primate Ayodele ya yi sabon hasashe gabannin bikin mika mulki na ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Ya bayyana cewa ba za a kafa gwamnatin wucin gadi ba a Najeriya kuma babu abun da zai hana rantsar da sabon shugaban kasa.
Asali: Legit.ng