Zaben Kano: Mun koya wa Ganduje darasin siyasa tsawon rayuwarsa, Jibrin

Zaben Kano: Mun koya wa Ganduje darasin siyasa tsawon rayuwarsa, Jibrin

  • Abdulmumini Jibrin Kofa ya ce fusatattun mambobin APC sun koya wa Ganduje darasin da ba zai manta ba a siyasa
  • Zababben ɗan majalisar tarayya a inuwar NNPP ya ce korar da Ganduje ya musu ta jawo APC rasa manyan kujerun Kano
  • NNPP mai kayan marmari ta samu nasarar lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris

Kano - Zababben ɗan majalisar tarayya karkashin inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Abdulmumini Jibrin, ya yi magana kan sakamakon zaben gwamnan Kano.

Jibirin ya bayyana cewa fusatattun mambobin jam'iyyar APC da suka tattara suka koma NNPP a Kano sun koya wa gwamna Abdullahi Ganduje darasin da ba zai manta ba a siyasa tsawon rayuwarsa.

Gwamna Ganduje da Kofa
Gwamnan Kano mai barin Gado, Ganduje da Abdulmumini Jibrin Hoto: Abdullahi Ganduje, Abdulmumini Jibrin
Asali: Facebook

Ɗan majalisar tarayya mai jiran gado ya yi wannan furucin ne yayin hira da kafar Channels tv a cikin shirinsu mai taken, 'Siyasa a yau'.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu: Jiga-jigan 'Yan Siyasa 3 Sun Hada Kai, Sun Fadi Wanda Suke So Ya Zama Shugaban Majalisa

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda NNPP ta lallasa jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen gwamna da 'yan majalisar jiha wanda ya gudana ranar 18 ga watan Maris a Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daily Trust ta rahoto Jibrin Kofa na cewa:

"Mai girma gwamna ba ya kaunar ganin da yawa daga cikinmu a inuwar APC saboda haka ya kai gwauro ya kai mari har sai da ya matsa mana muka bar jam'iyyar."
"Mu kuma muka haɗa kai muka koya masa darasin da ba zai manta ba a rayuwarsa ta siyasa. Mun tabbatar da cewa ba zai iya shakar numfashi ba a APC ta yadda ya jawo APC ta rasa 'yan majalisar tarayya. 18."
"Daga cikin waɗannan mambobin majalisar wakilan tarayyan da APC ta rasa har da guda 7 da Najeriya ke alfahari da su. Haka nan ya jawo wa APC ta rasa mambobin majalisar dokoki 34."

Kara karanta wannan

Watanni 2 Gabanin Ya Sauka Daga Mulki, Gwamnan PDP Ya Ƙara Jika Wa Zababɓen Gwamna Aiki

"Ina tabbatar muku wasu daga cikin waɗannan 'yan majalisar jihar suna da nagarta amma sun sha kaye ne saboda yaƙi ne da Ganduje, kuma suna inuwa ɗaya," inji shi.

Zan Yi Nesa da Abuja Bayan 29 Ga Watan Mayu, 2023, Inji Shugaba Buhari

A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai yi nesa da birnin Abuja idan ya gama wa'adinsa a watan Mayu

Yayin da ya karbi bakuncin babbar kwamishinar Birtaniya a Najeriya wacce ta je masa bankwana, Buhari, ya ce zumuncin kasashen biyu zai ɗore.

Kwamishinar Burtaniya ta taya shugaban kasa murna, inda ta ce tana takaicin barin Najeriya saboda kaunar da take wa ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262