PDP, LP, da NNPP Sun Hada Kai Domin Jagulawa APC Lissafi a Zaben Shugaban Majalisa
- Akwai ‘yan majalisai wakilan Najeriya barkatai da suke son tsayawa takarar shugabanci a 2023
- Jam’iyyun adawa sun fara kokarin amfanid a rabuwar kan ‘yan APC domin su fito da shugaba
- ‘Yan PDP, LP, APGA, YPP da NNPP su na ganin adadinsu ya kai su tsaida wanda zai jagorance su
Abuja - Jam’iyyun hamayya sun sha alwashin hada-kai da nufin samun baki daya a zaben shugabannin majalisar wakilan tarayya da za ayi a bana.
Rahoton Daily Trust ya ce ‘yan adawa a majalisar tarayyar sun cin ma wannan matsaya bayan wani taro da aka yi a otel din Transcorp Hilton a Abuja.
A karshen zaman da aka yi a daren Laraba, ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayya da ke majalisa sun amince su yi aiki tare domin su iya yin yadda suke so.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, wadanda suka halarci taron da aka yi a cikin dare sun hada da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP, LP, APGA, YPP sai kuma NNPP.
Za a hada-kan 'yan adawa
Da yake magana a taron, Dachung Bagos (PDP, Filato) ya shaidawa takwarorinsa ‘yan adawa sun samu nasarori da dama a majalisar nan da za ta shude.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Honarabul Bagos, idan aka samu hadin-kai musamman tsakanin sababbin masu shiga majalisa, za su iya samun abin da babu wanda ya yi tunani.
Shugaban ‘ya ‘yan jam’iyyar LP a majalisa, Fred Agbedi yana cikin wadanda suka gabatar da jawabi, ya yi wa sababbin shiga majalisa murnar cin zabe.
Wani rahoto na Punch ya tabbatar da cewa makasudin taron shi ne ‘yan adawa su yi amfani da yawan da suke da shi a majalisa, su fito da shugaba a 2023.
Kan APC ya rabu a takarar 2023
Zuwa yanzu fiye da mutum goma su ka nuna sha’awar kujerar da Femi Gbajabiamila yake kai, ‘yan adawa su na ganin za su iya amfani da rabuwar kan APC.
Honarabul Agbedi ya ce sakamakon zaben 2023 ya nuna ‘yan adawa za su iya tasiri, idan su ka dunkule.
Wakilan jam’iyyun PDP, LP, NNPP, SDP, APGA, ADC da YPP wanda duk su na da wakilci a majalisa ta goma sun nuna amanna da wannan shiri da ake yi.
Wa Tinubu zai ba mukamai?
Rahoto ya zo cewa jama’a sun koma tunanin wadanda Bola Tinubu zai ba mukami a Gwamnatinsa idan ya dare mulki, yau saura kwanaki 53 a canza shugaba.
Ana hangen irinsu Femi Gbajabiamila da Nasir El-Rufai a gwamnatin zababben shugaban na Najeriya. Akwai yiwuwar a zakulo wadanda ba ‘yan APC ba.
Asali: Legit.ng