Siyasar Kano: Abokin Karawar Ado Doguwa Ya Bukaci A Dakatar Da Yin Zaben Raba Gardama
- Salisu Yushau, dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudunwada a inuwar jam'iyyar NNPP ya garzaya kotu kan zaben raba gardama
- Yusha'u ya bukaci kotu ta dakatar da hukumar zabe INEC daga gudanar da zaben cike gurbin da ta shirya gudanarwa ranar 15 ga watan Afrilu
- Yushau Salisu, shi ne abokin karawar shugaban masu rinjaye a zauren majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa a zaben da INEC ta ce bai kammala ba
Kano - Dan takarar jam'iyyar NNPP na majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudunwada, Salisu Yushau, ya shigar da kara ya na neman a dakatar da hukumar zabe INEC gudanar da zaben raba gardama na mazabar, rahoton Daily Trust.
Yushau ne babban mai kalubalantar shugaban masu rinjaye a majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa, wanda aka fara ayyanawa a matsayin wanda ya lashe zaben, amma daga baya hukumar zabe ta janye sanarwar saboda dokar bambancin kuri'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hukumar zaben ta sanya ranar 15 ga Afrilu don gudanar da zabukan da su kammala ba a fadin kasar.
Bisa rashin amincewa da haka, dan takarar NNPP ya garzaya gaban kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisa da ke Kano ya na rokon kotun ta dakatar da INEC gudanar da zaben a yankin.
An kuma mika takardar koke ga shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu dauke da kwanan wata 3 ga Afrilu don janyo hankalin hukumar zaben kan batun karar.
Abin da yasa Yushau ke son a hana INEC yin zaben raba gardama a Kano
A takardar karar da hukumar INEC ta karba ranar 4 ga watan Afrilu kuma Daily Trust ta gani ranar Laraba, lauyan mai kara, Adegboyega Awomolo (SAN), ya ce la'akari da sashe na 24 (6) na dokokin zabe, 2022 su ka shigar da karar gaban kotun sauraren kararrakin zabe "su na neman a dakatar da hukumar zabe gudanar da zaben raba gardama da aka shirya a ranar 15 ga watan Afrilu 2023."
Da ya ke bayani, babban lauyan ya ce sashe na 24 (6) na dokar zabe 2022, ya haramtawa INEC gudanar da zabe a yankin saboda wanda ya ke karewa ya na kalubalantar matakin a gaban kotu, ya kara da cewa gudanar da zaben ka iya zama "karan tsaye ka kotun zaben wanda hakan cutarwa ne."
Da ya ke bayar da misalai da hukunce hukuncen kotun koli, lauyan dan takarar NNPP ya ce abu ne a bayyana a shari'a idan batu na gaban kotu, dole kowa ''ya mutanta kotu a kuma jira hukuncin da kotu za ta yi ba wai a cigaba da yadda aka tsara ba. Idan aka yi haka, karfin kotu, ya bata damar hukunta wanda bai mutanta hukuncinta akan lamarin ba."
Orji Kalu: Lokacin Da Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi
A wani rahoton mai alaka da wannan, Sanata Orji Kalu, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan Najeriya ya sanar da niyyarsa na shiga takarar shugabancin majalisar tarayya zubi na 10.
Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Jigon APC Ya Ce Peter Obi Ba Zai Yi Nasara A Kotu Ba, Ya Bada Dalili
Kalu wanda ke wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar, ya furta hakan ne a ranar Talata lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a majalisar.
Asali: Legit.ng