Jerin Gwamnonin da Suka Fara Ja'in Ja da Waɗanda Zasu Gaje Su Tun Kafin Miƙa Mulki

Jerin Gwamnonin da Suka Fara Ja'in Ja da Waɗanda Zasu Gaje Su Tun Kafin Miƙa Mulki

Wasu gwamnonin jihohi sun sha kashi a hannun manyan abokan hamayyarsu a zaben gwamnoni da mambobin majalisun jihohi da aka kammala ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Gwamnonin da hakan ta faru da su sun gama zangon mulki biyu na tsawon shekaru 8, amma duk da haka suka gaza samun amincewar mutanensu wajen tabbatar da ɗan takarar da suke so ya gaje su.

Bayan shan kashi a zaɓen da ya gabata, gwamnonin sun fara samun matsala da zababbun da zasu gaje su har an fara cece-kuce da nuna yatsa.

Ganduje Ortom da Ikpeazu.
Abdullahi Umar Ganduje, Samuel Ortom da Okezie Ikpeazu Hoto: Abdullahi Ganduje, Samuel Ortom
Asali: Twitter

Mafi yawan matsalolin da ke haɗa gwamnoni masu ci da masu jiran gadon sun shafi yanayin tafiyar da harkokin kuɗi na jihohi da wasu muhimman batutuwa.

Wasu daga cikin gwamnonin da muka tattaro muku sun ƙunshi, Abdullahi Ganduje na jihar Kano, Samuel Ortom na jihar Benuwai da Okezie Ikpeazu na Abiya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Ortom na jihar Benuwai

Gwamna mai barin gado a jihar Benuwai, Samuel Ortom, na PDP ya fara fuskantar ƙalubale daga zababben gwamna mai jiran gado, Hyacinth Aliya, na APC, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Manyan mutanen biyu sun fara nuna wa juna yatsa ne bayan wani kundi ya sulalo ya fito wanda zaɓaɓɓen gwamna ya aike wa shugaban kamfanin zuba hannun jari na Benuwai (BIPC), Alex Adum.

Gwamna Ikpeazu na Abiya

Gwamna mai barin gado na jam'iyyar PDP a Abiya, Okezie Ikpeazu, yanzu haka ya fara takun saƙa da zababben gwamna na Labour Party, Alex Otti, ya gargaɗi ya daina sa baki a gwamnatinsa.

A makon da ya shige, babbar kotun tarayya a Abuja ta garkame wasu asusunan banki mallakin jihar, lamarin da gwamna Ikpeazu ya zargi Otti da kulla manaƙisa.

Kara karanta wannan

Sirri Ya Fasu: An Gano Sunan Gwamnan Arewa da Wasu Mutum 2 da Tinubu Zai Ba Manyan Muƙamai Na Farko

Gwamna Ganduje na Kano

Kwanan nan aka ji gwamna Abdullahi Ganduje, na APC ya ja kunnen zababben gwamna, Abba Kabir Yusuf, na jam'iyyar NNPP bisa shiga sharo ba shanu tun kafin a rantsar da shi.

"Har yanzu nine gwamna," Ganduje ga Abba Gida-Gida bayan ya fitar da sanarwa yana mai gargaɗin duk wasu masu ba da bashin kuɗi su raba gari da gwamnatin Kano.

A wani labarin kuma Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban LP Na Ƙasa da Wasu Jiga-Jigai Uku

Rigingimun cikin gida a jam'iyyar LP ya ƙara tsananta bayan Kotu ta umarci shugaban jam'iyya da wasu shugabanni su daina ayyana kansu a matsayin jagororin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262