Hadimin Atiku Ya Kai Shugaban APC Kotu, Yana Bin Jam’iyya Bashin Naira Miliyan 120

Hadimin Atiku Ya Kai Shugaban APC Kotu, Yana Bin Jam’iyya Bashin Naira Miliyan 120

  • Daniel Bwala ya je kotun tarayya mai zama a garin Abuja, yana karar jam’iyyar APC mai mulki
  • Mai magana da yawun bakin na Atiku Abubakar a 2023 ya ce APC ta hana shi kudin aikin da ya yi
  • Bwala yana zargin wadannan kudi har N120m sun ki fitowa ne saboda ya sauya-sheka daga APC

Abuja - Daniel Bwala wanda yana cikin Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya yi karar Sanata Abdullahi Adamu a gaban kotu.

Daily Trust ta ce Daniel Bwala zai yi shari’a da shugaban APC na kasa ne bisa zargin cewa akwai wasu bashin kudi da yake bin Jam’iyyar mai mulki.

A cewar Bwala wanda Lauya ne, kudin aikin da ya yi wa APC kafin ya sauya-sheka a 2023 sun taru har sun kai Naira miliyan 120, ba a biya shi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 da Suka Auka Matsalar Zabe Bayan Yin Fito Na Fito da Buhari a Kan Canjin Kudi

Wannan shari’a mai lamba CV/2009/2023 ta na gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Rokon Lauyoyin Daniel Bwala

Lauyoyin Bwala sun bukaci kotu ta umarci jam’iyyar APC da shugaban ta na kasa, Abdullahi Adamu da su biya kamfaninsa bashin da ke kan su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce takardun kotu da aka gani sun nuna cewa Lauyoyin da suke kara sun gabatar da batutuwan da sun fi karfin hurumin kotun tarayyar.

Shugaban APC
Taron shugabannin APC Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Kudi sun haura N120m

Kamfanin tsohon jigon na APC ya ce ya yi wa jam’iyyar aiki a jihohin Kuros Riba, Osun, Kaduna, Benuwai, Ondo da Abuja, amma ba a sallame shi ba.

Bwala ya na ikirarin kudin aikin da ya yi wa jam’iyyar APC a shari’a tara da aka yi a Najeriya ya kai N135,000,000.00, wanda har ya hakkinsa bai fito ba.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu Ta Karbe N725m da Kadara a Hannun Tsohon Shugaban Hukumar NIMASA

Da ya zanta da manema labarai, Vanguard ta rahoto Kakakin kwamitin PCC na jam’iyyar PDP yana cewa watakila sauya-shekarsa ta jawo hakan.

Lauyan yake cewa babu mamaki saboda ya bar jam’iyya mai mulki ya shiga PDP, ya kuma taya Atiku Abubakar yin kamfe, shiyasa aka hana shi kudinsa.

A cewar ‘dan siyasar, ya yi kokarin bin duk wata hanyar lalama domin ganin hakkinsa sun fito, amma hakan ya ci tura, saboda haka ya je kotu.

Jita-jitar Sanusi Lamido Sanusi

A wani rahoto da mu ka fitar, an ji cewa wasu wadanda Bola Tinubu yake jin shawararsu, sun dage Sanusi Lamido Sanusi ya koma babban bankin CBN.

Babu mamaki zababben Shugaban ya yi kokarin korar Godwin Emefiele idan an rantsar da shi musamman ganin yunkurinsa na canza kudi daf da zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng