Tinubu Zai Nada Mutanen da Ba 'Yan APC Ba A Gwamnatinsa, Jigo

Tinubu Zai Nada Mutanen da Ba 'Yan APC Ba A Gwamnatinsa, Jigo

  • Jigon APC ya yi ikirarin cewa zababben shugaban kasa zai ɗauko wasu mutane da ba yan jam'iyya ba ya basu muƙami
  • Nicolas Felix, ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi takara a APC, ya ce burin Tinubu ya kafa gwamnatin haɗin kan kasa
  • Yace ba ruwan Tinubu da jam'iyyar mutum, abinda zai duba kwarewa da gogewa da cancantar yin aiki

Abuja - Tsohon ɗan takarar da ya nemi tikitin shugaban kasa a inuwar APC, Nicolas Felix, ranar Talata, ya ce shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, zai ba da mamaki.

Felix ya ce Tinubu zai naɗa zakakuran mutane masu hazaƙa a gwamnatinsa bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, kamar yadda Punch ta rahoto.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jigon APC mai mulki ya yi wannan furucin ne yayin hira da Arise TV ranar Talata 4 ga watan Afrilu. Tinubu zai duba kwarewa da cancanta a naɗe-naɗensa ba ruwansa da jam'iyya, inji shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Kuma Shugaba a Majalisar Dattawa Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

Ya bayyana cewa kowane ɗan Najeriya yana da haƙƙi ba tare da la'akari da jam'iyar siyasar da ya hito ba. Ya kara da cewa idan baku manta ba Tinubu ya ce zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"Asiwaju mutum ne mai saka alheri, mai saka aiki tuƙuru, akwai 'yan Najeriya waɗanda ba mambobin APC masu basira, gogewa da cancanta. Na san zai duba har wajen APC ya zakulo mutane."
"Amma ina da yaƙinin zai buɗe hannunsu ya ce 'ina son kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa, idan kana PDP, Labour Party ko sauran jam'iyyu, mu duka yan Najeriya ne."

Jigon siyasan ya roki 'yan Najeriya da su haɗa hannu da Bola Tinubu domin dawo da Najeriya kan turba.

A cewarsa duk lokacin da aka zabi sabon shugaban kasa ana tsammanin kowane ɗan ƙasa ya ba da gudummuwa a yi aiki tare matuƙar dai mutum ba ɗan son rai bane.

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Kulla-Kular Da 'Yan Siyasa Ke Yi Domin Samun Shugabancin Majalisa

Tarihi ba zai manta da kai ba, Gwamna Wike ya yabi Ortom

A wani labarin kuma Bayan Gama Zaɓen 2023, Gwamna Wike Ya Faɗi Gwamnan Arewa 1 Tilo Da Ya Kafa Tarihi a Najeriya

Gwamnan jihar Ribas ya yabi takwaransa na jihar Benuwai, Samuel Ortom, bisa goyon bayan kudu da ya nuna a zaben shugaban ƙasa.

Wike ya ce duk da Ortom ya sha kashi a kokarin ƙaƙaba magajinsa da kuma Sanatan da ya nema, shi ne cikakken wanda ya samu nasara a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262