Ribas Zata Goyi Bayan Wanda APC Ke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai, Wike

Ribas Zata Goyi Bayan Wanda APC Ke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai, Wike

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kara bullo da sabon abinda ka iya jawo kace nace a cikin jam'iyyar PDP
  • Wike, wanda ya taimaka wajen faɗuwar Atiku, ya ce Ribas zata zauna inuwa ɗaya da APC a majalisar wakilai
  • Ya ce sabuwar majalisar da za'a kafa na bukatar jajirtattu kuma masu gogewa su jagorance ta

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin cewa jihar zata goyi bayan duk wanda jam'iyyar APC ta gabatar a matsayin wanda take son ya zama kakaki a majalisar wakilai ta 10.

Wike ya faɗi haka ne yayin da mataimakin kakakin majalisa na yanzu, Ahmed Idris Wase, ya jagoranci tawagar abokan aikinsa suka kai masa ziyara har gidan gwamnati a Patakwal.

Wase da Wike
Ribas Zata Goyi Bayan Wanda APC Ke So Ya Zama Kakakin Majalisar Wakilai, Wike Hoto: @Ahmed Idris Wase
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi bayanin cewa jam'iyyar PDP ta ci kujerun yan majalisar wakilan tarayya 11 daga cikin 13 da jihar ke da su, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Miyagun Yan Daba Sun Kusa Sheƙe Ɗan Takarar Gwamnan APC a 2023

Ya jaddada cewa waɗannan 'yan majalisu 11 zasu mara baya ga duk wanda APC ta bi hanyar maslaha ta tsayar da shi ya zama kakakin majalisar wakilan tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"A yanayin da muke ciki yanzu, dole ne mu faɗi gaskiya cewa zamu goyi bayan jagororin jam'iyyarku a matakin ƙasa. Ba zan goyi bayan kowa ba daga ko ina ya fito idan ba APC ba."

Wa ya kamata ya zama kakakin majalisa ta 10?

Gwamnan ya ƙara da cewa masu gogewa da kwarewar daidaita al'amurorin kasar nan ya kamata a gabatar a matsayin shugabannin majalisar dokokin tarayya ta 10.

A rahoton Vanguard, Wike ya ce:

"Alal misali kai (Wase) kana da kwarewa, ba abinda muke bukata illa wannan kwarewa a majalisar wakilai, hakan zai daidaita komai a majalisar, saboda haka baka bukatar wani ƙarin haske."

Kara karanta wannan

Sanatan APC Ya Fasa Kwai, Ya Bayyana Kulla-Kular Da 'Yan Siyasa Ke Yi Domin Samun Shugabancin Majalisa

A wata sanarwa da kakakinsa, Kelvin Ebiri, ya fitar, gwamna Wike ya ƙara jaddada godiyarsa ga gwamnonin APC da sauran jagorori, waɗanda suka ga ya dace mulki ya koma kudu.

An Gano Sunayen Mutum 3 da Tinubu Ke Shirin Ba Manyan Muƙamai

A wani labarin kuma Wasu Sabbin rahotanni sun fallasa sunayen 'yan gaban goshin Tinubu da zai ba manyan muƙamai

Wasu majiyoyi sun sun faɗi wanda ke kan hanyar zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa da tawagar ɓangaren tattalin arziƙin ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262