Gwamna Wike Ya Bukaci 'Yan Adawar Jihar Rivers Su Marawa Zababben Gwamnan Jihar Baya
- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya buƙaci ƴan adawa jihar da su ba zaɓaɓɓen gwamnan jihar goyon baya
- Gwamna Wike ya nemi waɗanda suka sha kashi a zaɓen gwamnan jihar da su haƙura da zuwa kotu
- Gwamna Wike ya shawarce su da su zo a haɗa hannu da su domin ciyar da jihar ta Rivers gaba
Jihar Rivers- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya buƙaci jam'iyyun adawar jihar da suka sha kashi a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris da su marawa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Sir Siminalayi Fubara, baya.
Gwamnan ya bayyana cewa tun da an kammala zaɓuka, dukkanin ƴan siyasan da suke son cigaban jihar da zuciya ɗaya da su rungumi sasanci domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin su. Rahoton Leadership
Gwamnan ya nemi jam'iyyun adawa da suke son zuwa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da su sake tunani, su mayar da hankali wajen cigaban jihar fiye da burin su na ƙashin kan su.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ina kira ga waɗanda zasu je kotun sauraron ƙarar zaɓe da su haƙura, su bari jihar Rivers ta cigaba. Ku goyawa zaɓaɓɓen gwamna baya domin ciyar da jihar Rivers gaba."
Wike yayi nuni da cewa wasu daga cikin waɗanda ke ƙoƙarin zuwa gaban kotun sun san cewa mutanen jihar Rivers ba su zaɓe su ba, saboda yadda suka damfari gwamnatin jihar maƙudan kuɗi har $50m.
Saboda haka zuwan su kotu baya da wata ma'ana face sai domin kawo wa zaɓaɓɓen gwamnan katsalandan kamar yadda suka yiwa gwamnatin sa. Rahoton The Sun
“Da ace bamu mayar da hankali ba, da an ɗauke mana hankali wanda shine abinda suke so su yi yanzu, ta hanyar tabbatar da cewa sun kawo wa zaɓaɓɓen gwamnan katsalandan. Ina son na sharwarce ka (Fubara) kada kaji tsoro." Inji shi
Ana Shirin Rantsar da Sabon Shugaban Kasa, Wata Jam’iyya Ta Kai Tinubu Kotu
A wani labarin na daban kuma, wata jam'iyya ta sake kai ƙarar zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya, Bola Tinubu, a gaban kotu.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen rantsar da ɗan takarar.
Asali: Legit.ng