Hirar Waya Da Aka Bankado: Babban Faston Najeriya Bishop Oyedepo Magantu Kan Tattaunawarsa Da Obi
- Bishop David Oyedapo ya karyata zargin tattaunawa da Peter Obi na jam'iyyar LP don taimaka ma sa cinye kuri'un kudu maso yamma gabanin zaben 2023
- Martanin Oyedapo na zuwa ne biyo bayan wata hirar waya da ke yawo tsakaninsa da Peter Obi a kafafen watsa labaran zamani
- A cewar Oyedapo, ba wanda ya taba fada ma sa abun da zai yi kuma ba wanda zai gwada hakan har sai in ya mutu ko ya shiga aljanna
Mammalakin Cocin Living Faith, Bishop David Oyedapo, ya karyata ikirarin tattaunawa da dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi don taimaka ma sa da kuri'un Jihar Kwara gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Daily Trust ta ruwaito cewa Oyedapo lokacin da ya ke magana a cocinsa ranar Lahadi, 2 ga watan Afrilu, ya ce bai taba tallata wani dan takara ba a fadin kasar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Martanin Oyedapo na zuwa ne kasa da awa 24 bayan People Gazette, wani gidan jaridar yanar gizo ya wallafa wata hirar waya tsakanin malamin da Peter Obi na Jam'iyyar LP.
A hirar, an jiyo Peter Obi na rokon goyon bayan Oyedapo ya taimaka ma sa da kuri'ar kiristocin da ke kudu maso yamma da na Jihar Kwara, jihar da malamin ya fito.
A cikin tattaunawar wadda da yawa daga cikin magoya bayan Peter Obi ciki har da mai mai magana da yawun ofishin ObiDatti Media, Diran Onifade, suka fitar, tsohon gwamnan Anambra sun roki Oyedapo da ya yi magana ga mabiyansa.
An jiyo shi ya na cewa:
"Baba, ina so kayi magana da mutanen ka na kudu maso yamma da kuma kwara, kiristocin kudu maso yamma da na kwara.
“Ba Za a Rantsar Da Tinubu Ba:” Magoyin Bayan Peter Obi Ya Fasa Ihu a Bidiyo, Ya Hana Jirgin Sama Tashi
"Wannan yaki ne tsakanin addini. Kamar yadda na sha fada: idan na yi nasara, ba za ku yi dana sanin goyon bayan da kuka ba ni ba."
Sai dai, da ya ke martani kan hirar wayar, Oyedapo ya ce bai taba magana da wata kungiya a madadin wani dan siyasa ba.
Bishop din ya ce:
"Ba wanda ya taba gaya min abin da zan fada a duniyar nan. Ban taba tallata wani ko na yi magana a madadin shi ba kuma ba zan yi haka ba har na koma ga Allah.
"Babu wata jam'iyyar siyasa da bata zo wajena don neman addu'a da shawara ba. Na ba su shawara, wasu, ba su dauka ba.
"Wanda suka dauki shawara, sun ga sakamako; wanda suka ce a'a, za su gani (ya yi dariya). Idan ka sake zuwa, zan sake baka shawara, ba zai canja ba."
'Yes Daddy': Dan Majalisar Kano Sagir Koki Ya Kwaikwayi Peter Obi Bayan Ganawarsa Da Kwankwaso
Zababben dan majalisar Kano Municipal, Sagir Koki, ya kwaikwayi kalaman Peter Obi dan takarar shugaban kasa na LP, yayin hirarsa da babban Fasto, Bishop David Oyedepo.
Asali: Legit.ng