Hadimin Buhari Ya Tabbatar da Wani Minista Ya Yi Murabus, Ya Faɗi Suna
- Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya tabbatar da batun murabus ɗin karamin ministan albarkatun man Fetur
- Ahmad ya ce Ministan ya aje aiki ne domin bin dokar zaɓe wacce ta umarci wanda zai nemi takarar siyasa ya yi murabus
- Timipre Sylva, ya rike kujerar gwamna a jihar Bayelsa, yanzun ya sake komawa domin tsaya wa takara a zaɓe mai zuwa
Abuja - Mai baiwa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkonin sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad, ya tabbatar da cewa ƙaramain ministan albarkatun man Fetur, Temipre Sylba, ya yi murabus.
A wata gajeruwar sanarwa da ya fitar a shafinsa na Tuwita ranar Jumu'a, Ahmad ya ce Ministan ya yi murabus ne domin ya shiga tseren takarar gwamna a jihar Bayelsa.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa INEC ta shirya gudanar da zaben gwamnan jihar ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Ƙaramin ministan albarkatun Man fetur kuma tsohon gwamna a jihar Bayelsa, H.E. Timipre Sylva, ya yi murabus daga kan muƙaminsa domin ya shiga zaɓen gwamna na gaba a jihar."
Mista Sylva ya rike kujerar gwamnan Bayelsa karkashin inuwar jam'iyyar PDP daga watan Mayu, 2007 zuwa watan Afrilu, 2008 lokacin da aka soke zaɓen da ya samu nasara.
Kakakin majalisar dokokin jihar a wancan lokacin, Werinipre Seibarugo, ne ya maye gurbinsa har lokacin da aka canja zabe Sylva ya ƙara nasara a watan Mayu, 2008.
A watan Janairu, 2012, Kotun koli da ake wa laƙabi da Kotun Allah ya isa ta rushe gwamnatinsa. Bayan haka ya sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Bayan sauya shekarsa ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi karamin ministan albarkatun man Fetur ranar Laraba 21 ga watan Agusta, 2019.
Jam'iyyar LP Ta Dakatar da Shugabanta Na Kasa
A wani labarin kuma Labour Party ta shiga rigingimun cikin gida kamar PDP, ta dakatar da shugaban jam'iyya na kasa
LP a matakin gumduma daga jihar Edo, ta ce ta dakatar da Julius Abure, ne bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.
Sai dai sakataren jam'iyya na kasa ya maida martani mai zafi, ya ce kwansutoshin ya tsara yadda za'a iya tuge shugaban LP na ƙasa.
Asali: Legit.ng