Majalisa Ta 10: Dan Majalisa Daga Jigawa Ya Shiga Cikin Masu Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Na Tarayya
- Dan majalisar tarayya mai wakiltar Mallammadori/Kaugama ya shiga jerin ma su neman takarar shugabancin majalisar wakilai
- Dan majalisar ya ce yana da yakinin za a bawa yankin Arewa maso Yamma ko Arewa ta Tsakiya damar shugaban majalisar
- Ya kuma roki jam'iyyar APC da ta zabi yankinsa saboda tasirin yawan ma su kada kuri'a da kuma irin goyon bayan da suka bai wa Tinubu har ya lashe zabe
FCT, Abuja - Wani karin dan majalisar wakilai na tarayya, Abubakar Yalleman, ya shiga jerin ma su zawarcin kujerar shugabancin majalisar wakilai ta 10, rahoton The Punch.
Yalleman yana wakiltar Mallammadori/Kaugama da ke Jihar Jigawa a majalisar kuma shine shugaban kwamitin tsaro na majalisar wakilan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dan majalisar bayyana cewa, tsarin shiyya na shugabancin majalisar na jam’iyyar APC mai mulki, shi zai nuna wanda zai ci gaba da jan ragamar majalisar dattawa da na majalisar tarayya, shine zai fayyace mukaman da ‘yan majalisar za su nemi takara.
Ya kuma roki jam’iyyar APC ta mayar da kujerar shugaban majalisar wakilai zuwa yankin Arewa, yana mai cewa hakan zai kara inganta daidaito rabon mukaman siyasa a kasar.
Yalleman yace duk da kasancewar ba kundin mulkin kasa ne ya zo da tsarin karba-karba ba a rabon mukaman siyasa ba, amma kusan haka al'adar da kasar ta kasance kanta ne.
A wata zantawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba, dan majalisar yace:
“Ina so in fada muku cewa zan tsaya takarar shugabancin majalisar wakilai zubi ta 10, idan shugaban jam’iyyarmu ta APC ya bai wa shiyyar da na fito Arewa-maso-Yamma.
''Abin da zan yi in na samu nasara zama shugaban majalisar, zan tafi tare da kowa duk da bambancin jam'iyya, addini, kabila da yare. Zan tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin matakan gwamnati, yan majalisa, bangaren zartarwa da na shari'a.''
Yalleman yace yana da yakinin cewa za a bada takarar ga yankin Arewa maso Yamma ko Arewa ta Tsakiya.
Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya fito daga Kudu maso Yamma, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima, ya fito daga Arewa maso Gabas.
Arewa maso yamma ne ta fi yawan kuri'u don haka ta cancani kujerar kakakin majalisa - Yelleman
Yalleman, yayinda yake bayyana dalilan shi yace, yankin Arewa maso Yamma, shi ne ya fi yawan masu kada kuri’a, kamar yadda INEC ta fitar.
Ya kara da cewa masu zabe a yankin sun bada goyon baya har a kai nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu.
Dan majalisar yace duk jihohi bakwai da ke Arewa maso Yamma, da suka hada da Jigawa, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kano, Kebbi da Sokoto Tinubu ya samu nasara a jihohin Jigawa da Zamfara kadai, yayinda ya zo na biyu a sauran jihohin 5.
Yalleman yace a Arewa maso Yamma, Jigawa ba ta samar da kakakin majalisar wakilai ba.
Ya kara da cewa daga 1999 shugabannin majalisar sune Salisu Buhari da Ghali Na’Abba daga Jihar Kano; Aminu Masari daga Katsina; da Aminu Tambuwal daga Sokoto.
Gwamnonin Ondo da Kogi sun goyi bayan Wase ya zama kakakin majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa Rotimi Akeredolu, gwamnan Ondo da Yahaya Bello, gwamnan Kogi, gwamnan jihar Kogi sun goyi bayan dan Arewa ta Tsakiya ya zama kakakin majalisa zubi ta 10.
Kamar yadda Vanguard ta rahoto, Akeredolu da Yahaya Bello sun bayyana hakan ne Ahmed idris Wase, mataimakin kakakin majalisa ya ziyarce su.
Asali: Legit.ng