Bola Tinubu Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya a Ranar Cika Shekara

Bola Tinubu Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya a Ranar Cika Shekara

  • Bola Ahmed Tinubu ya aike da sako ga yan Najeriya bayan cikarsa shekara 71 a duniya ranar Laraba
  • Zababben shugaban ƙasan ya ce karo na farko yan Najeriya sun ba shi kyautar da ba'a taba ba shi ba a rayuwarsa
  • Ya ce ya shirya sake gina ƙasar nan domin kowane ɗan Najeriya su samu sa'ida da salama

Abuja- Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya shirya tsaf domin sake gina kyakkyawar Najeriya da kuma sabunta, "fatan mutanen cikin ƙasar nan."

The Cable ta rahoto cewa Tinubu ya yi wannan furucin ne a sakon da ya aike wa 'yan Najeriya ranar cikarsa shekara 71 a duniya ranar Laraba.

Tinubu
Bola Tinubu Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya a Ranar Cika Shekara Hoto: The Cable
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya ce 'yan Najeriya sun ba shi kyautar ƙarin shekara da ba'a taɓa ba shi watau damar da suka ba shi na jagorantar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Zai Cika Alkawarin Barin Najeriya Da Yayi Idan Tinubu Yaci Zaben Shugaban Kasa

A watan Fabrairu, hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ƙuri'u 8,794,726.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu da ƙuri'u 6,984,520 yayin da Peter Obi na LP wanda ya ba mutane mamaki ya tashi da kuri'u 6,101,533 a matsayi na uku.

Zaɓaɓɓen shugaban kasan ya ce alkawurran da ya ɗauka ba wai tsatsuniyoyi bane na dabarun cin zaɓe, zai cika su kowa ya gani a ƙasa. Rahoton Channels Tv

A kalamansa:

"Duba da alfarmar da aka mun, ba zan yi wani dogon zance ba, na gama da duk wata kyauta domin an bani kyauta mafi girma a rayuwata."
"Damar zama kujera lamba ɗaya kuma damar jan ragamar cika muradai da kuma tabbatar da mafarkin 'yan Najeriya ya zama gaskiya."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Yace Shugaban PDP Na Kasa Tinubu Ya Yi Wa Aiki, Ya Tona Asirin Abinda Ya Faru

"Maimakon haka zan yi amfani da wannan damar na ƙara baku kalamai na da muhimman aikin da muka tasa a gaba na sake gina ƙasar nan da kuma sabunta kyakkyawan fatan mutanen Najeriya."

Tinubu ya ci gaba da cewa,

"Waɗan nan alkawurran da na ɗauka ba wai daɗaɗan kalamai ne na yaudarar goyon baya bane, suna nufin babban aikin da na tasa a gaba na inganta Najeriya, kowa ya amfana ko ka zaɓe ni ko baka zaɓe ni ba."

Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Jindadin 'Yan Sanda Ta Ƙasa

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabon shugaban hukumar jindaɗin ƴan sanda ta ƙasa (PSC)

Solomon Arase tsohon sufeta janar na ƴan sandan Najeriya (IGP), ya kama aiki gadan-gadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng