Gombe: APC Na Binciken Yan Majalisa Kan Zargin Yiwa Jam’iyya Zagon Kasa
- Jam'iyyar APC a jihar Gombe tana kaddamar da bincike a kan wasu mambobinta kuma yan majalisar tarayya
- Ana zargin Sanata Bulus Amos da dan majalisar wakilai, Yunusa Ahmad Abubakar da cin dunduniyar janm'iyyar
- APC ta ce yan majalisar sun taimakawa jam'iyyar adawa a zaben gwamna da na yan majalisar jiha da ya gudana
Gombe - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Gombe ta kafa wani kwamiti don binciken Sanata Bulus Amos da wani dan majalisar wakilai, Yunusa Ahmad Abubakar.
APC ta kafa kwamitin ne a ranar Talata, 28 ga watan Maris domin ya binciki yan majalisar kan zarginsu da ake da yiwa jam'iyyar zagon kasa, Daily Trust ta rahoto.
Laifin da ake zargin yan majalisar sun aikata
Sakataren APC a gudunmar Lubo/Difa/Kinafa, Samaila Ali, ne ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai a garin Lubo da ke karamar hukumar Yamaltu/Deba ta jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ali ya ce jam'iyyar na zargin cewa Yunusa Abubakar ya hada kai da jam'iyyar adawa a lokacin zaben gwamna da na majalisa a jihar.
Ya ce suna sane da cewar dan majalisar tarayyan ya umurci sauran mambobin jam'iyyar da magoya bayansa da su zabi wata jam'iyya ta daban ba APC ba, rahoton The Sun.
Hakazalika, shugaban APC na gudunma a garin Bamban na karamar hukumar Balanga da ke jihar, Muhammadu Kaka, ya ce shugabannin gudunmar sun kafa kwamitin mutum biyar don binciken sanata mai wakiltan Gombe ta kudu, Bulus Amos.
Kaka ya ce an kafa kwamitin ne kan zargin Amos da cin dunduniyar jam'iyyar a zaben da ya gabata.
Ya yi zargin cewa Sanata Amos ya ki shiga dukkanin kamfen din jam'iyyar gabannin zaben da ya gabata sannan kuma cewa ya umurci magoya bayansa da kada su zabi jam'iyyar aa zaben da ya gabata.
Jam'iyyar ta bayyana cewa za a binciki yan majalisar biyu masu ci tare da sauran mambobin APC a jihar, wadanda ake zargin sun taimakawa jam'iyyun adawa a zaben da ya gabata a jihar.
Kiristan kudu ne ya cancanci zama shugaban majalisar dattawa, inji dan majalisa
A wani labari na daban, dan majalisa mai wakiltan mazabar Egbeda/Ona Ara ta jihar Oyo, Akin Alabi ya bayyana cewa kiristan kudu ne ya fi cancanta ya zama shugaban majalisar dattawa.
Alabi ya ce akwai bukatar yin hakan saboda zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun kasance duk Musulmai ne.
Asali: Legit.ng