Jerin Duka Shugabannin PDP 9 da Aka Yi Rabuwar Tsiya da Su Daga 1999 zuwa 2023
- Irinsu Audu Ogbeh, Adamu Mu’azu, Modu Sheriff, Uche Secondus sun yi mulki babu dadi a PDP
- A tsawon shekaru 25 da kafa PDP, an yi shugabanni kusan 20, wasu ba a ji dadin zama da su ba
- Iyorchia Ayu shi ne na karshen wanda ake neman a kare da rigima da shi a gidan Wadata a PDP
Abuja - Wannan rahoto yana kunshe da mutanen da suka jagoranci Jam’iyyar PDP a cikin rigingimu, a karshe dai aka tunbuke su daga kujerarsu.
Alex Ifeanyichukwu Ekwueme ne ya fara shugabantar PDP a 1998. Daga wancan lokaci zuwa yanzu, an samu shugabannin da aka yi fada da su.
1. Solomon Lar (1998-1999)
A wani rahoto na Daily Trust, an ji cewa tsamin da alakar Solomon Lar da Olusegun Obasanjo tayi, ya jawo aka yi waje da shugaban jam’iyyar PDP a 1999.
2. Barnabas Gemade (1999-2001)
Barnabas Gemade ya gaji Lar a ofis, amma shi ma bayan kusan shekaru biyu ya samu sabani da shugaban kasa na lokacin, bai iya zarcewa a ofis a 2001 ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Audu Ogbeh (2001-2005)
Abubuwa sun fara tafiya da Audu Ogbeh tiryan-tiryan, daga baya sukar da yake yi wa gwamnatin tarayya ta jawo wani mutumin na Benuwai ya yi murabus.
4. Prince Vincent Ogbulafor (2008 - 2010)
Vincent Ogbulafor ya karbi jagorancin PDP NWC ne a 2008, amma Umaru Musa Yar’adua yana rasuwa aka tsige shi bayan ya nuna mulki zai tsaya a Arewa.
5. Dr. Okwesileze Nwodo (2010)
Tsohon Gwamnan Enugu, Dr. Okwesileze Nwodo bai dade a matsayin shugaban PDP ba aka tunbuke shi, a lokacinsa an yi ta samun sabani da Gwamnoni.
6. Dr. Bamanga Tukur (2012-2014)
A lokacin Bamanga Tukur ne PDP ta rasa wasu jiga-jigan ta zuwa jam’iyyar APC, a karshe dai dole ya sauka daga kujera a 2014 bayan an matsa masa lamba.
7. Adamu Mu'azu (2014-2015)
Ahmad Adamu Mu’azu ya maye gurbin Bamanga Tukur daga Arewa maso gabas, amma ganin APC ta doke PDP a zaben 2015, aka dage sai da aka canza shi.
7. Ali Modu Sheriff (2015-2016)
Tun da Ali Modu Sheriff ya karbi shugabancin PDP ake rikici, a maimakon ya karasa watanni ukun Adamu Muazu, sai ya nemi ya zarce a mulki, da rigima aka rabu.
8. Uche Secondus (2017-2021)
Sai da kotu ta tsige Prince Uche Secondus sannan ya yarda ya mika ragamar jam’iyyar adawa ta PDP a 2021, daga shugabancin riko, ‘dan siyasar ya ji dadin ofis.
9. lyorchia Ayu (2021 - 2023)
A cikin shugabannin PDP da ba ayi rabuwar mutunci da su ba akwai Iyorchia Ayu idan ta tabbata an kore shi, tun da Atiku Abubakar ya samu takara ake sa-in-sa.
Shugabannin jam’iyyar PDP na kasa
A wani rahoto da muka taba kawowa, kun ji a shekaru 23 da kafuwar jam’iyyar PDP a Najeriya, ta yi shugabanni da-dama, fiye da goma daga Arewa suka fito.
Dr. Alex Ekwueme ne ya fara rike wannan kujera a matsayin rikon kwarya. An samu shugabanni irinsu Vincent Ogbulafor da Uche Secondus daga Kudu.
Asali: Legit.ng