Gwamna Ortom Ya Hakura Da Kayen Da Yasha a Kujerar Sanata
- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ya aminta da kayen da yasha a zaɓen sanata na ranar 25 ga watan Fabrairu
- Gwamnan ya bayyana cewa ya janye ƙarar da ya shigar domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen
- Titus Zam ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen kujerar sanata ta Benue ta Arewa maso Yamma, shine ya kayar da Ortom
Jihar Benue- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ya karɓi kayen da ya sha a zaɓen kujerar majalisar dattawa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton The Cable
Ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Titus Zam, ya tiƙa Ortom da ƙasa inda ya samu nasarar lashe kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Yamma.
Bayan bayyana sakamakon zaɓen, Ortom yace zai yi nazari kan sakamakon kafin ya fitar da bayanin sa. Bayan sati biyu da yin hakan sai ya bayyana cewa jam'iyyar sa ta shirya ƙalubalantar zaɓen a gaban kotu saboda maguɗin da aka tafka.
An Tafka Magudi: Dan Takarar Gwamnan PDP Yaki Yarda Da Kaddara, Zai Kalubalanci Sakamakon Zabe a Kotu
Sai dai, a ranar Talata, Ortom ya bayyana cewa ya janye ƙarar sa akan Zam domin a samu zaman lafiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wani jawabi da gwamnan yayi a birnin Makurdi na jihar, yace duk da cewa an samu kura-kurai a zaɓen, mutum babu abinda zai samu sai wanda Allah ya ƙaddaro masa.
Ya nuna godiyar sa kan damar da aka ba shi ta jagoranci inda yace ya tabbatar da cewa a gwamnatin sa ya samar da gaskiya da adalci. Rahoton The Nation
A kalamansa:
"A lokacin da nake gudanar da mulkin jihar nan, na tabbatar da cewa akwai gaskiya, adalci da bin doka da oda. Duk da cewa akwai hujjoji ƙuru-ƙuru na maguɗi waɗanda suka haɗa da rashin ɗora sakamako kan yanar gizo a zaɓen sanatan Benue ta Arewa maso Yamma,"
"Na yanke shawarar janye ƙarar da na shigar a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen. Kamar yadda aka koyar da mu a littafin Bible cewa kowa rabon sa yake samu."
Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara
“Bari kuma na ƙara da cewa, hukuncin da na yanke na janye ƙarar daga kotu na yi shine domin samun zaman lafiya, kuma bai shafi sauran ƙararrakin da ƴan takarar jam'iyyar PDP suka shigar ba."
Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Cross Rivers, Yayi Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP na jihar Cross Rivers yayi fatali da sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Ɗan takarar ya lissafo kura-kuran da aka tafka a zaɓen inda ya bayyana matakin da zai ɗauka na gaba.
Asali: Legit.ng