Masu Ruwa da Tsaki Na Mazaɓar Ayu Sun Mamaye Sakatariyar PDP Ta Kasa

Masu Ruwa da Tsaki Na Mazaɓar Ayu Sun Mamaye Sakatariyar PDP Ta Kasa

  • Masu ruwa da tsakin PDP daga jihar Benuwai sun dira babbar Sakatariyar jam'iya ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Hakan ta faru ne awanni bayan sauya shugaban PDP da mataimakinsa na shiyyar Arewa, Iliya Umar Damagun
  • PDP na fama da rigingimun cikin gida tun kafin zaben shugaban kasa, rikicin ya ci gaba da ruruwa har zuwa bayan zaɓe

Abuja - Masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP daga gundumar Igyorev, ƙaramar hukumar Gboko, jihar Benuwai sun isa babbar Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa da ke Abuja.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa jiga-jigan PDP daga mahaifar Iyorchia Ayu yanzu haka sun fara jawabi a wurin taron 'yan jarida da suka kira.

Mutanen garinsu Ayu.
Masu Ruwa da Tsaki Na Mazaɓar Ayu Sun Mamaye Sakatariyar PDP Ta Kasa Hoto: Vanguardngr
Asali: UGC

Daga cikin masu ruwa da tsakin har da mambobin PDP a gundumar Igyorev, yankin da shugaban jam'iyya na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya fito.

Kara karanta wannan

"Dama Na Faɗa" Gwamna Wike Ya Maida Martanin Kan Maye Gurbin Shugaban PDP Na Kasa

A yau Talata, jam'iyyar PDP ta sanar da sauke Ayu da kumamaye gurbinsa da mataimakinsa na shiyyar arewa, Ambasada Damagun a matsayin shugaban riko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan baku manta ba, wani tsagin shugabannin jam'iyyar a gundumar sun sanar da cewa sun dakatar da Ayu daga kasancewa mamban PDP bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.

Matakin dai ya haddasa cece-kuce da martani daga bangarorin daban-daban na jam'iyyar PDP yayin da jam'iyyar ke jimamin shan kaye a babban zaben da aka kammala.

Mai magana da yawun Ayu, a wata sanarwa da ya fitar, yace gunduma ba ta da hurumin dakatar da mamban kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC).

A cewarsa majalisar koli ta jam'iyyar PDP (NEC) kaɗai ke da ikon dakatarwa ko ɗaukar mataki kan wani mamban NWC.

Awanni bayan haka aka ji babban abokin adawar Ayu kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi caraf ya ce ya ji daɗi da gundumar Ayu ta sanar da dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaban PDP Na Kasa Ya Sauka Daga Kujararsa, An Maye Gurbinsa Nan Take

Sihiri Aka Mun Na Bar Kwankwaso Na Koma Wurin Ganduje, Ali Artwork

A wani labarin kuma Jarumin Kannywood, Ali Artwork, ya ce Asiri aka masa shiyasa ya bar tafiyar Kwankwaso zuwa ta Ganduje a Kano

Fitaccen Ɗan kwamedin kuma jarumin Kannywood, yace sai da aka matsa da addu'o'u da neman magani sannan Allah ya karya asirin ya samu sauki.

A halin yanzun yanata kokarin sake komawa Kwankwasiyya amma magoya baya na ganin ya ci musu mutunci da rashin ɗa'a a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262