Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana

Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana

  • An shaidawa zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya cika alkawuran yakin neman zabensa da zarar an rantsar da shi
  • Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zabensa kuma ministan kwadago, Barista Festus Keyamo (SAN) ne ya yi rokon
  • A cewar Keyamo, cika alkawarin da ya daukarwa yan kasa lokacin yakin neman zabe ne kawai zai iya sanyawa ya siye zuciyar yan adawa

Karamin ministan kwadago, Festus Keyamo wanda kuma ya rike mukamin mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana abin da ya zama dole ubangidansa ya yi bayan an rantsar da shi ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin tuwita wanda Legit.ng ta hango ranar Litinin, 27 ga watan Maris, Keyamo ya ce dole Tinubu ya bawa yan adawa kunya ta hanyar fara gudanar da kyakkyawar gwamnati.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Keyamo, Tinubu
Abin Da Ya Zama Dole Tinubu Ya Fara Yi Da Zarar An Rantsar Da Shi, Festus Keyamo Ya Bayyana. Hoto: Festus Keyamo (ESQ), Bola Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa dole tsohon gwamnan na Jihar Lagos ya fara da cika alkawuran da ya daukarwa yan Najeriya don karyata ma su shakkarsa.

Ga abin da Keyamo ya rubuta:

''Na gano cewa babu wani abu da za mu iya yi a kafafen sadarwa (na zamani ko tsofaffin) don sanya wanda ba su zabe mu ba su yarda da mu face gudanar da kyakkyawar gwamnati kamar yadda Tinubu ya alkawarta. Da zarar an rantsar da shi, dole a tsaya da magana a kuma fara aiki!''

Obidients sun yi martani ga rubutun Keyamo

Sai dai, magoya bayan jam'iyyun adawa sun mayar da martani a sashen bayyana ra'ayi don sukar rubutun Keyamo.

Omowale_Cee ya ce:

''Ranka ya dade kai ministan Najeriya ne, na fahimci lokacin neman aiki shi ne ka na cikin wani, amma kada ka bata tsohon aikinka, na fahimci ka na bukatar sabon mukami amma ka mayar da hankali a wanda ka ke da shi yanzu.''

Kara karanta wannan

Ku Tallafawa Mahaifina, Ba Zai Iya Shi Kadai Ba, Yar Tinubu Ta Roki Yan Najeriya

Slyvia_Ikeji na cewa:

''Festus, in kun dama ku mayar da ita Dubai amma tabbas wata rana za mu karbi hakkin mu kuma dole a yi adalci. Barawo ba zai iya sace min mota kuma saboda ya kula da ita sosai a ce in bar ma sa ba. Karyane. Dole ku dawo mana da hakkin nan.''

OlalekeSteven:

''Duk da na goyawa takarar Peter Obi baya, abin da na ke yawan fada shi ne ''Asiwaju na da shekaru hudu don ya nuna kansa ga yan Najeriya, bayan shekara hudu za mu tantance ko mu za mu shiga irin da mu ke ciki a wannan gwamnati''.

Obasanjo da Obi sun hadu a jihar Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya sadu da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, a Awka, jihar Anambra a filin tashi da saukan jiragen sama.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164