Ayu Bai Nemi Zaman Lafiya Ba Idan Ya Yi Fatali da Umarnin Kotu, Bode George

Ayu Bai Nemi Zaman Lafiya Ba Idan Ya Yi Fatali da Umarnin Kotu, Bode George

  • Rigingimu sun kara ɗaukar zafi a cikin babbar jam'iyyar hamayya PDP bayan umarnin Ƙotu
  • Bode George yace idan Ayu ya yi watsi da umarnin Kotu to ba ya neman zaman lafiya a cikin jam'iyya
  • Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan babbar Kotun Makurɗi ta dakatar da Ayu daga shugabancin PDP

Yayin da ake tsaka da rikici a jam'iyyar PDP, Babban jigo, Bode George, yace shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, na neman karin rigima ne idan ya yi watsi da umarnin Kotu.

A ranar Litinin, wata babbar Kotu mai zama a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai ta yanke hukuncin cikin shari'a, ta umarci Ayu ya dakatar da bayyana kansa a matsayin shugaban PDP.

Bode George
Ayu Bai Nemi Zaman Lafiya Ba Idan Ya Yi Fatali da Umarnin Kotu, Bode George Hoto: Bode George
Asali: UGC

Alƙalin Kotun mai shari'a W.I. Kpochi, ya yi wannan umarnin a ƙara mai lamba MHC/85/2023, wanda mamban PDP daga jihar Benuwai, Terhide Utaan, ya shigar yana tuhumar Ayu da PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Yace Shugaban PDP Na Kasa Tinubu Ya Yi Wa Aiki, Ya Tona Asirin Abinda Ya Faru

Sa'ilin da ya bayyana a cikin shirin Politics Today na Channels tv, Mista George, mataimakin shugaban PDP, ya shawarci Ayu ya bi umarnin Kotu don gujewa matsala.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan har Kotu da Alkali sun yanke hukunci, kamata ya yi mashawarcin shari'a na PDP ta ƙasa da Ayu su garzaya Kotun su roki Alkali cewa wannan umarnin bai dace ba saboda kaza da kaza."
"Idan baku yi haka ba kuma kuka yi watsi da umarnin Kotun, to baku nemi zaman lafiya ba, kuna neman jawo sabon matsala."

A wani bangaren matakan dawo da zaman lafiya da magance rikicin cikin gida, Bode George, ya buƙaci a kwantar da hankali kuma mambobin PDP su haɗa kansu.

A cewarsa, duk gidan da kawuna suka rabu ba zasu kai labari ba. Ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ai Yanzu Aka Fara – Fitaccen Gwamna Ya Ragargaji Shugaban Jam’iyya

"Abinda nake cewa shi ne iyayenmu da suka kafa jam'iyyar nan sun yi bayani dalla-dalla cewa duk wanda ya zama shugaban ƙasa bai kamata ya fito shiyya ɗaya da shugaban jam'iyya ba."
"Ina tuna kalaman Ayu cewa idan har ɗan takarar shugaban kasa ya fito daga arewa zai yi murabua, amma bai yi ba, wannan kuskuren an riga an tafka shi."

Gwamna Umahi Ya Tona Asirin Ayu, Ya faɗi Yadda Ya Yi wa APC aiki

A wani labarin kuma Gwamnan Umahi Yace Shugaban PDP Na Kasa Tinubu Ya Yi Wa Aiki, Ya Tona Asirin Abinda Ya Faru

Gwamnan jihar Ebonyi, yace ƙin murabus din Ayu kamar yadda gwamnonin G5 suka nema ba karamin taimakawa APC da Bola Tinubu ya yi ba.

David Umahi, ya bayyana haka ne yayin da ya je Ribas kaddamar da muhimmin aikin Wike, yace Ayu ya yi wa APC aiki a ɓoye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262