Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Hadimin Gwamna Matawalle a Zamfara

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Hadimin Gwamna Matawalle a Zamfara

  • Tsagerun 'yan bindiga sun je har gida sun sace mashawarcin gwamnan Zamfara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Ma’aji
  • Babban ɗan hadimin gwamnan ya ce maharan sun hauro gidansu ta katanga, suka tilasta masa kai su ɗakin mahaifinsa
  • An yi koƙarin jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan Zamfara, SP Muhammad Shehu amma ba'a same shi ba

Zamfara - Wasu 'yan bindiga da ake zaton yan fashin daji ne sun yi garkuwa da mai baiwa gwamna Bello Matawalle shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Ma’aji.

Tribune ta ce yan bindigan dajin adadi mai yawa sun kutsa gidan hadimin gwamnan da farkon awanni ranar Asabar a Anguwar Mareri, cikin kwaryar birnin Gusau.

Alhaji Ibrahim Ma’aji.
Mai baiwa gwamnan Zanfara shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Ma’aji Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Babban ɗan hadimin gwamnan, Lukman Ibrahim, ya tabbatar da labarin garkuwa da mahaifinsa har gida a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamna Matwalle Ya Karbi Kaddara, Ya Amince Da Kayen Da Ya Sha, Ya Nemi Wata Alfarma Wajen Al'ummar Zamfara

A cewar Lukman, mahaifinsa na cikin ɗakinsa lokacin da maharan suka diro cikin gidan ta katanga. A kalamansa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina cikin ɗaki lokacin da na ji wani ya diro cikin gidanmu, nan take na fito na duba waye kawai yan bindiga suka cafke ni."
"Suka tilasta mun na kaisu ɗakin mahaifina kuma daga nan, suka yi awon gaba da shi zuwa mafakarsu da ba'a sani ba."

A rahoton Dailypost, Lukman ya kara da cewa tun da wuri-wuri aka kai rahoton abinda ya faru ga hukumar yan sanda domin ɗaukar mataki kan yuwuwar ceto hadimin gwamnan.

Yayin da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ba'a sami lambarsa ba, wayar tarho ɗinsa a kashe har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yan Jagaliya Sun Kaddamar da Hari a Ofishin APC dake Zamfara, Biyu Sun Tafi Lahira

An Tsinci Gawar Ɗan Takarar Gwamnan Imo Na Jam'iyyar LP

A wani labarin kuma Bayan dawowa daga wurin taro a Abuja, ɗan takarar gwamnan LP a jihar Imo ya mutu a gidansa na jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen ɗan siyasan ya rasu ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Jumu'a a gidansa.

An ce tuni ya sayi Fam din tsayawa takara na jam'iyyar LP gabanin zaben fidda gwani a jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262