Mansur Sokoto Ya Yi Wa Dauda Lawal Nasihar Ratsa Zuciya Bayan Cin Zaben Gwamna

Mansur Sokoto Ya Yi Wa Dauda Lawal Nasihar Ratsa Zuciya Bayan Cin Zaben Gwamna

  • Sheikh Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi wa Dr. Lawal Dauda Dare nasiha bayan ya ci zabe
  • Malamin ya fadawa zababben Gwamnan ya rungumi kowa, ya nemi na kwarai su zagaye mulkinsa
  • Idan Lawal Dare ya shiga ofis ya guji yin wasa da zikirori da neman addu’o’i na neman taimako

Zamfara - Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya kai ziyara zuwa wajen Dr. Lawal Dauda Dare wanda ya yi nasara a zaben Gwamnan jihar Zamfara.

Babban malamin hadisin Musuluncin ya tunatar da zababben Gwamnan da kissar Sayyidina Abubakar RA da yaron gidansa bayan yi wa Nana Aisha kazafi.

A wannan bidiyo da yake yawo a shafin Twitter, an ji Mansur Ibrahim Sokoto yana fadakar da Dauda Lawal cewa tun da an samu nasara, ka da a koma fada.

Kara karanta wannan

‘Yan Kwanaki Da Cin Zaben Majalisa, Shehi Ya Koma Gabatar da Tafsirin Azumi a Kano

Malamin yake cewa da zarar an rantsar da mutum a kan mulki, babu maganar ‘wane nawa ne ko wane ba nawa ba ne', ya ce daga yanzu kowa ya zama na shi.

Shugabanci akwai tsoro

Mulki akwai dadi, amma Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya ce a kiyama zai zama abin tsoro, domin Allah zai tambayi Gwamna mai jiran gado abin da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin ya jawo Hadisin Manzon Allah da yake cewa shugabanci amana ce, nadama a kiyama sai ga wanda ya dauka bisa cancanta, yana tsare hakkin al’umma.

Lawal Dare Dauda
Lawal Dare Dauda wajen kamfe Hoto: Lawal Dauda
Asali: Facebook

An ji malamin jami’ar ta Usman Danfodiyo da ke garin Sokoto yana cewa al’umma su na ganin Lawal Dauda ya cancanta ya jagorancin Zamfara a zaben 2023.

Shawarwari masu muhimmanci

Wata shawara da aka ba zababben gwamnan shi ne ya rike shugabanci da kyau, kuma ya jawo na kwarai; ya dauko masu fada masa gaskiya ba son ransu ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Minista Ya Rubutawa DSS Wasika, Ya Nemi a Cafke Peter Obi da Baba Ahmed

Haka zalika, Mansur Sokoto ya fadawa Gwamnan mai-jiran gado ya tabbata ya rika bada mukami inda ya cancanta, ya rika yin nadin kujeru lura da cancanta.

Ga wadanda ba su da wata kwarewa illa siyasa, Shehin yake cewa akwai hanyoyin yin sakayya a ofis, sannan ya nuna masa dole ya rike zikirori safe da yamma.

Malamin ya fadawa Lawal ya nemi taimakon Allah, ya guji gadara idan ya na neman nasara, sannan ya roki Allah neman dacewa, sannan mutane su taimaka masa.

Zababben 'dan majalisa mai tafsiri

A rahotonmu na yau, an ji cewa a cikin watan nan, Abdulhakeem Kamilu Ado ya rasa mahaifinsa ana shirin zabe, a karshe ya samu tikitin shiga zabe, ya yi nasara.

Matashin da yake koyarwa a jami’a ya zama zababben 'dan majalisar Wudil da Garko, a jiya Abdulhakeem Ado ya fara tafsirin Ramadan a masallacin Jami’ar KUST.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng