Murna Ya Barke Yayin Da Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Oyetola Na APC Da Adeleke Na PDP
- Kotun daukaka kara a Abuja ta jingine hukuncin da kotun sauraron karar zaben gwamnan jihar Osun ta yi na soke nasarar Gwamna Ademola Adeleke
- A hukunci da mafi rinjayen alkalai suka bada, kotun zaben ta yanke cewa Adeleke bai ci zabe ba kuma ta ayyana Gboyega Oyetola na APC a matsayin wanda ya lashe zaben
- Amma, Adeleke bai gamsu da hukuncin kotun zaben ba kuma ya kallubalanci hukuncin a kotun daukaka kara, daga bisani ta jadada nasararsa
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta jadada nasarar Gwamna Ademola Adeleke a zaben gwamna na watan Yuli a jihar Osun.
A cewar Channels Television, kotun daukaka karar ta jingine hukuncin zaben gwamnan na jihar Osun da ta soke nasarar gwamnan.
Abin da yasa kotu ta mayar da Ademola Adeleke a matsayin gwamnan Osun
Idan za a iya tunawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 16 ga watan Yuli a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar INEC, Adeleke ya samu kuri'u 403,371 inda ya doke Oyetola wanda ya samu kuri'u 375,027 a lokacin yana gwamna mai ci.
Dan takarar na APC Oyetola ya yi watsi da sakamakon zaben ya kuma kallubalanci nasarar Adeleke a kotun sauraron karar zabe.
A Janairun wannan shekarar, kotun zaben, a wani hukunci da mafi rinjayen alkalan suka bada, ta soke zaben da ta ba wa Adeleke nasara ta kuma jadada nasarar Oyetola.
Abin da ke faruwa kan Ademola Adeleke, Gboyega Oyetola, APC, PDP, Zaben 2023
Amma, hukuncin da alkalai marasa rinjaye suka bayar da bakin Mai shari'a B. Ogbuli, sun ce Adeleke shine ya lashe zaben.
Adeleke da PDP, ba su gamsu da hukuncin kotun karar zaben ba, suka garzaya kotun daukaka kara.
A ranar Litinin, 13 ga watan Maris, kotun daukaka karar ta saurari jawabi daga bangarorin biyu sannan ta jingine bada hukunci.
Amma, yayin bada hukuncinta a ranar Juma'a, kotun daukaka kara ta jingine hukuncin kotun karar zaben ba.
Amma, kotun ta tafi hutu na mintuna 5 kuma za ta bada hukuncinta bayan ta dawo.
Jam'iyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Katsina, zata tafi kotu
A bangare guda, jam'iyyar hamayya ta PDP, a jihar Katsina ta ce ba ta yard da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na 2023.
Shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku/Lado, Mustapha Inuwa, ya sanar wa manema labarai hakan a ranar Litinin.
Asali: Legit.ng