PDP Ta Lashe Karamar Hukumar Karshe da INEC Ta Sanar a Jihar Abiya
- Labour Party ta kawo karshen mulkin jam'iyyar PDP na tsawon shekaru 24 a jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya
- INEC ta ayyana dan takrar gwamna a inuwar LP, Alex Otti, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala ranar Asabar
- An kai ruwa rana yayin tattara sakamakon zaɓen wanda sai yau aka sanar da sakamakon karamar hukumar ƙarshe
Abia - Daga ƙarshe hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana sakamakom zaben gwamna daga ƙaramar hukumar Obingwa ta ƙarshe a jihar Abiya.
Daily Trust ta rahoto cewa INEC ta sanar da sakamakon Obingwa, karamar hukumar da ta haddasa ruɗani da kace-nace a cibiyar tattara sakamako da ke Umuahia, babban birnin jihar Abiya.
Sakamakon ya nuna ɗan takarar gwamna a inuwar Peoples Democratic Party (PDP), Okey Ahaiwe, ya lallasa babban abokin karawarsa na Labour Party, Alex Otti, da ƙuri'a mafi rinjaye.
Cikakken sakamakon zaben gwamna daga Obingwa LG
ADC 37
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
ADP 19
APC 721
APGA 1445
APM 18
APP 383
BP 113
LP 3776
NNPP 41
NRM 48
PDP 9962
PRP 12
SDP 55
YPP 3101
ZLP 48
INEC ta faɗi wanda ya lashe zaben gwamnan Abiya
Bayan karban wannan sakamakon, INEC ta ayyana dan takarar Labour Party, Alex Otti, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Abiya.
Mista Otti, tsohon Darakta a Diamond Bank Plc, ya samu kuri'u 175,467, ya lallasa takwaransa na PDP kuma tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Okey Ahaiwe, wanda ya samu kuri'u 88,529.
Baturen zaben jihar shugaban jami'ar fasaha ta tarayya da ke, Owerri, jihar Imo (FUTO), Farfesa Nnenna Otti, ne ya sanar da wanda ya samu nasara bayan gama tattara sakamako.
Yanzu Yanzu: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Zanga-Zanga Ke Gudana a Ofishin INEC Kan Ayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Wata Jiha
Tribune ta ce an samu tsaiko a tattara sakamkon zaben gwamnan Abuya har ta kai ga dakatarwa bayan rigingimun da suka biyo baya kan zargin maguɗi.
A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Tona Asiri, Ya Faɗi Abinda Gwamnonin PDP 5 Suka Ƙulla a Zaben Tinubu
Gwamnan jihar Ribas ya ce babu lokacin da gwamnonin G5 suka zauna suka yamke goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.
Maimakon haƙa Wike ya bayyana abu ɗaya da suka cimma wa game da zaven shugaban kasan da aka kammala.
Asali: Legit.ng