An Shiga Zullumi Bayan INEC Ta Ki Amincewa Da Sakamakon Zaben Jihohi 2, Ta Bayyana Dalili

An Shiga Zullumi Bayan INEC Ta Ki Amincewa Da Sakamakon Zaben Jihohi 2, Ta Bayyana Dalili

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Jihar Abia da Enugu saboda kurakurai
  • A cewar hukumar zaben, sakamakon zaben da aka gabatar ya saba da adadin ma su zaben da aka tantance
  • Idan za a iya tuna wa INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben Abia da Enugu saboda wasu kurakurai

FCT, Abuja - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta na kasa, INEC, ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan Jihar Abia da Enugu saboda wasu kurakurai.

A rahoton jaridar New Telegraph, hukumar zaben ta ce sakamakon bai yi daidai da adadin ma su zaben da aka tantance ba.

Shugaban INEC
INEC ta ki amincewa da sakamakon zaben gwamnan Abia da Enugu. Hoto: INEC
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Daga karshe: INEC za ta ci gaba da tattara sakamakon zaben wasu jihohi biyu yau dinnan

Meyasa INEC ta yi watsi da sakamakon Abia da Enugu

Tun da farko an ruwaito cewa an dakatar da tattara sakamakon zaben a jihohin Abia da Enugu saboda wasu kurakurai.

INEC ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan tsaikon tattara sakamako da aka samu a karamar hukumar Obingwa da ke Jihar Abia.

Haka nan, a Enugu, an dakatar da tattara sakamakon zabe a kananan hukumomin Nkanu ta gabas da Nsukka da ke jihar biyo bayan zargin magudi da yan takarar jam'iyyar PDP da LP su ka yi.

Yadda ake ciki game da zaben Abia, Enugu, INEC, zaben 2023, kudu maso gabas

Hukumar zaben ta kuma bayyana cewa za a sake duba sakamakon zaben a kananan hukumomin da ta soke, ta na mai cewa za ayi abin da ya dace.

A cewar majiyar:

''Za a sanar da sakamako nan ba da jimawa ba. An gama duba sakamakon Abia da Enugu.''

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Kammala Nazari Kan Sakamakon Zaben Gwamnoni 28, Ta Ɗauki Mataki Kan Jihohi 2

Majiyar ta kuma gano cewa hukumar zaben ta kuma umarci a sake duba sakamakon zaben 18 ga watan Maris a Jihar Enugu.

An samu tashin hankali a Abia da Enugu bayan dakatar da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihohin biyu.

Samuel Ortom Ya Sha Kaye Zaben Sanata, Dan Takarar APC Ya Lashe Zaben

A wani rahoton, kun ji cewa Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai ya gamu da rashin nasara a zaben sanata na mazabar Benue Arewa maso Yamma da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu inda dan takarar APC, Cif Titus Zam ya ci zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164