Jerin Abubuwa 5 Da Obi Ya Bukaci Kotun Zabe Ta Yi Masa A Yayin Da Ya Ke Kallubalantar Nasarar Tinubu
FCT, Abuja - Peter Obi, dan takarar jam'iyyar LP na shugaban kasa, ya shigar da kara don kalubalantar nasarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC a zaben 25 ga watan Fabrairun 2023.
Obi wanda ya yi na uku a zaben, ya shigar da kara don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa a kotun sauraron karrarakin zabe a Abuja da yammacin Litinin, 20 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga jerin abu 5 da dan takarar jam'iyyar Labour ke nema a kotun:
1. A soke takarar Tinubu da Shettima
Obi ya roki kotun da ta ayyana Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a matsayin haramtattun yan takara a zaben 25 ga wata.
Ya kuma roki kotun da ta sanar da cewa Tinubu bai samu mafi rinjayen halastattun kuri'u ba a zaben.
Na karshe, Obi ya bukaci kotun da ta bayyana shi (Obi) a matsayin wanda ya cika sharuddan da za a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 25 ga watan Fabrairu bayan kwashe haramtattun kuri'u daga na Tinubu
2. Kwace nasarar Tinubu saboda rashin samun kaso 25 a Abuja
A bukata ta biyu, tsohon gwamnan Jihar Anambra ya bukaci kotu ta kwace nasar Tinubu.
Ya kafa hujja da rashin samun Tinubu kaso daya bisa hudu na kuri'ar da aka kada a babban birnin tarayya, Abuja.
3. A soke zabe sannan a umarci INEC ta gudanar da sabo
A bukatarsa ta uku, wanda ya bari a matsayin zabi, Obi ya roki kotu da ta soke zabe gaba daya.
Ya kuma bukaci kotu ta umarci INEC ta sake gudanar da sabon zabe bayan ta soke wancan.
4. A bayyana ni a matsayin zababben shugaban kasa
A bukatarsa ta hudu wanda ita ma ke a matsayin zabi, Obi ya yi ikirarin shi ya lashe zaben kuma ya na so kotun ta bayyana shi a matsayin zababben shugaban kasa.
Dan takarar jam'iyyar LP ya yi ikirarin cewa shi ya lashe mafi rinjayen halastattun kuri'un da aka kada a zaben 25 ga watan Fabrairu ya kuma bukaci kotu ta sanar da shi a matsayin zababben shugaban kasa ta kuma umarci INEC ta ba shi shaidar cin zabe.
Ya bukaci kotu ta soke shaidar cin zabe da aka baiwa Tinubu bisa ''kuskure''.
5. A soke zabe
A bukatarsa ta biyar, wani karin zabi, Obi ya bukaci kotu ta soke zabe a kuma sake wani zaben.
Ya kafa hujja cewa ya mika bukatar ne saboda an gudanar da zabe ba tare da bin dokokin zabe ba.
Asali: Legit.ng