Sarkin Musulmi Ya Aike da Sakon Taya Murna Ga Zababben Gwamnan Sakkwato
- Sarkin Musulmai a Najeriya ya ta ya zababben gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, murnar samun nasara a zaɓe
- Alhaji Sa'ad Abubakar ya aike da wannan sako ne ta hannun wakilan da ya aika don ta ya murna ga jagoran APC na jihar
- Gwamna mai jiran gado na APC ya gode wa Sarkin Musulmi wanda ya kira da Uba ga kowane ɗan Najeriya
Sokoto - Mai Alfarma Sarkin musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa'ad Abubakar IIII, ya taya zababben gwamna Sakkwato murna.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Sultan ya taya Alhaji Ahmed Aliyu na APC murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan da aka kammala a jihar Sakkwato.
Abubakar ya taya murnar ne ta hannun wakilan da ya aika zuwa ga jagoran APC, Sanata Aliyu Wamakko, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Sambo Junaidu, wazirin Sakkwato ranar Talata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Wamakko, Bashar Abubakar, ya fitar, Sarkin Musulmi yace ba'a taɓa zabe cikin zaman lafiya kamar wannan ba a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A matsayin mu na shugabanni, zamu ci gaba da da aiki kafaɗa da kafaɗa da sabon gwamna domin kawo ci gaba g al'ummar mu da jihar Sakkwato baki ɗaya," inji shi.
Mai Alfarma Sarkin Musulmai ya ƙara da cewa haka Allah ya tsara Aliyu ne zai samu nasara a zaɓe, inda ya bayyana cewa, "Allah ke ba da mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so."
Basaraken ya kuma roki Allah ya taimaki zababben gwamna kuma Ya kare shi wajen tafiyar da al'anuran jihar Sakkwato domin goben mazauna ta yi kyau.
Da yake na sa jawabin, gwamna mai jiran gado, Aliyu ya gode wa Sultan kana ya ayyana shi da Uba ga kowa. Ya kuma yi alƙawarin zai yi aiki da kowa wajen cika manyan kudirorinsa guda 9.
Pulse ta rahoto Aliyu na cewa:
"Ina tabbatar wa baban mu, Sultan cewa mun sha alwashin jawo kowa a cikin gwamnatinmu domin tabbatar da mutane sun samu sauyi mai kyau."
Gwamnan Nasarawa ya yi jawabin farko bayan lashe zabe
A wani labarin kuma Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana abinda ya yi wa mutanen da basu kaɗa masa kuri'u ba a zaben da ya gabata
Gwamnan, ɗan takarar jam'iyyar APC ya samu nasarar tazarce kan kujerarsa, ya ce ya yafe wa duk wanda ya yaƙe shi lokacin zaɓe.
Asali: Legit.ng