2023: Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP, Ta Kwace Mulkin Jihar Benuwai
- Gwamnan Samuel Ortom na jam'iyyar PDP ya gaza kawo wa jam'iyyarsa kujerar gwamna a zaben ranar Asabar
- Ɗan takarar APC kuma babban malamin Majami'a, ne ya samu nasara da kuri'u mafiya rinjaye
- Wannan dai ya tabbatar da cewa kujerar gwamnan Benuwai ta bar hannun PDP ta koma tsagin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasa
Benue - Ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Hyacinth Alia, ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai bayan kammala tattara sakamako.
Rabaran Fada Alia, babban Malamin Coci, ya samu kuri'u 473,933, ya lallasa babban abokin karawarsa na jam'iyyar PDP mai mulkin jihar, Titus Uba, wanda ya samu kuri'u 223,913.
Ɗan takarar gwamna a inuwar Labour Party, Herman Hembe, shi ne ya zo na uku da kuri'u 41,881 a sakamakon da INEC ta sanar ranar Litinin, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Baturen zaben INEC kuma shugaban jami'ar fasaha ta tarayya da ke Minna jihar Neja, Farfesa Faruk Kuta, ne ya sanar da sakamakon zaben ranar Litinin 20 ga watan Maris, 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake jawabi a cibiyar tattara sakamako ta INEC da ke Makurdi, babban birnin jihar, ya ce daga cikin kananan hukumomi 23, Rabaran Alia ya samu nasara a guda 17, Uba ya ci 4, sai kuma Hembe da ya samu ɗaya tal.
Haka nan Farfesa Kuta ya ce ya bayyana Alia a matsayin wanda ya samu nasara ne dogaro da tanadin kundin dokokin zabe da kuma sharudda INEC.
Kafin wannan nasara, jihar Benuwai da ke arewa maso tsakiya a Najeriya na karƙashin mulkin PDP na gwamna Samuel Ortom, mamba a tawagar G-5, kamar yadda Punch ta rahoto.
An yi hasahen PDP da LP ne zasu yi goyayya a zaben gwamnan jihar saboda Ortom mamban PDP ne amma ya goyi bayan ɗan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.
INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Bauchi
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta samu nasara a zaben gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya
Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, ya yi nasara a zaben gwamna a yunkurinsa na tazarce kan kujerarsa bayan lallasa babban abokin adawarsa na APC.
Asali: Legit.ng