INEC Ta Dage Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

INEC Ta Dage Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ɗage tattara sakamakom zaɓen gwamnan jihar Adamawa
  • Hukumar ta ɗage tattara sakamakon zaɓen ne bayan hatsaniya ta ɓarke kan sakamakon zaɓen da ya fito daga wata ƙaramar hukuma
  • Wakilan jam'iyyu sun yi cacar baki kan sahihancin sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar inda wasu ke ganin an yi muru-muru a cikin sa

Jihar Adamawa- Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), a jiya da daddare ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa har sai ziwa yau da rana.

An dai ɗage tattara sakamakon zaɓen ne biyo bayan hargitsin da ya ɓarke akan sahihancin sakamakon zaɓen da ya fito daga ƙaramar hukumar Fufore. Rahoton Daily Trust

Yakubu
INEC Ta Dage Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa Hoto Vanguard
Asali: Facebook

Baturen tattara sakamakon zaɓe na jihar, Farfesa Muhammad Lamin Mele, ya bayyana sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 20 cikin 21 kafin hatsaniya ta ɓarke tsakanin wakilan jam'iyyu kan sahihancin sakamakon da ya fito daga Fufore.

Kara karanta wannan

Bayan Sake Komawa Kan Kujerar Sa, Gwamnan PDP Ya Sha Wani Babban Alwashi Kan Bola Tinubu

Wakilin jam'iyyar APC, Usman Mauludu, yayi zargin cewa an sauya sakamakon zaɓen da ya fito daga Fufore.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan sai jami'in hukumar INEC mai kula da zaɓuɓɓuka a jihar, Yunus Hudu, sai ya ɗage tattara sakamakon zaɓen har zuwa ƙarfe sha biyu na ranar yau.

An dai ɗage tattara sakamakon zaɓen ne duk da adawar da wakilan jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin tsohon ƙaramin ministan lafiya na ƙasa, Aliyu Idi Hong, suka yi inda suka haƙiƙance kan cewa dole sai an cigaba da tattara sakamakon zaɓen.

Jami'an tsaro sun harba hayaƙi mai sa hawaye da harbi kan ƴan daba ɗauke da sanduna waɗanda suka taru kusa da cibiyar tattara sakamakon zaɓen suna takalar masu ababen hawa.

Ƴan daban dai sun lalata wasu motoci a wajen.

Ana Jiran Sakamakon Zaben Gwamnan Kano Yayin da Aka Samu ‘Inconclusive’ a Kebbi

Kara karanta wannan

Karin Bayani: INEC Ta Fara Ɗora Sakamakon Zaben Gwamnoni da Na'urar BVAS

A wani labarin na daban kuma, rahoto ya zo cewa ana ta zaman dakun sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kano, yayin da aka samu zaɓen da bai kammala ba a jihar Ƙebbi.

Hukumar INEC tace zaɓen gwamnan jihar Kebbi bai kammalu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng