2023: APC Ta Lashe Mafi Rinjayen Kujeru a Majalisar Dokokin jihar Ondo

2023: APC Ta Lashe Mafi Rinjayen Kujeru a Majalisar Dokokin jihar Ondo

  • Jam'iyyar APC ta yi gagarumin nasara a zaben majalisar dokokin jihar Ondo wanda aka yi a ranar Asabar
  • APC mai mulki ta yi nasarar lashe kujeru 22 cikin 26 na majalisar jihar ta kudu a zaben ranar Asabar, 18 ga watan Maris
  • Babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP ta tashi da sauran kujerun guda hudu

Ondo - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dokokin jihar Ondo a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, jaridar Thisday ta rahoto.

A sakamakon da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana a jihar, APC ta lashe kujeru 22 cikin 26 na mazabun da ke fadin kananan hukumomi 18 a jihar.

A nata bangaren, babbar jam'iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP) ita ta lashe sauran kujerun guda hudu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Lallasa APC, Ta Lashe Rumfuna 2 a Gidan Gwamnatin Kaduna

Logon jam'iyyar APC
2023: APC Ta Lashe Mafi Rinjayen Kujeru a Majalisar Dokokin jihar Ondo Hoto: THISDAYLIVE
Asali: Twitter

Jihar Ondo na daya daga cikin jihohi takwas da ba a yi zaben gwamnoni ba a ranar Asabar saboda Gwamna mai ci, Mista Oluwarotimi Akeredolu (SAN), zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu ne a 2024.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon zaben da aka sanar ya nuna karara cewa fafatawan da aka yi a zaben na ranar Asabar ya kasance tsakanin APC da PDP ne a fadin rumfunan zabe 3,933 da gudunmar siyasa 203 a fadin kananan hukumomin jihar.

APC ta lashe kujeru 22 inda ta rasa biyu a Akoko ta kudu maso yamma, daya a Akoko ta arewa maso yamma sannan dayan a karamar hukumar Akure ta kudu.

Jerin yan majalisar da basu samu nasarar zarcewa ba

Hakazalika, hudu daga cikin yan majalisa takwas masu ci wadanda ke neman zarcewa sun sha kaye a zaben.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kwace Kayan Zabe Sun Kona a Wata Jihar Kudu, Jami'an INEC Sun Tsere

Sun hada da Tomide Akinribido (Ondo ta yamma 1 PDP); Favour Tomomewo (Ilaje 2, ADC); Hon. Taofeeq Muhammed (Akoko ta arewa maso yamma 2, APC) and Toluwani Borokini (Akure ta kudu1, APC).

Yan majalisar da suka yi nasara

Sai dai kuma yan majalisa hudu masu ci sun yi nasarar zarcewa. Sun hada da Oluwole Emmanuel Ogunmolasuyi (Owo 1 APC/shugaban masu rinjaye); Oladiji Olamide (Ondo ta gabas APC).

Sauran sune Ololade Gbegudu (Okitipupa 11, APC); da Abayomi Akinruntan (Ilaje 1, APC) wanda ke komawa a karo na uku.

Yan majalisa mata uku za su kasance a majalisar dokokin jihar ta 10 kasancewar mata yan APC sun yi nasara a mazabun Owo 1, Idanre da Ilaje 2, rahoton The Cable.

Sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomin jihar Neja

A wani labari na daban, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa ta fara tattara sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomin jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng