Yanzu Yanzu: Shugaban PDP Da Aka Yi Wa Mugun Duka a Ebonyi Ya Mutu

Yanzu Yanzu: Shugaban PDP Da Aka Yi Wa Mugun Duka a Ebonyi Ya Mutu

  • Babban jagoran PDP a karamar hukumar Ezza ta arewa a jihar Ebonyi, Peter Nweke, ya kwanta dama
  • Yan daban siyasa ne suka far ma shugaban na PDP a rumfar zabensa inda suka yi masa dukan kawo wuka
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin iinda ta ce tuni ta shiga bincike don kamo miyagun tare da hukunta su

Ebonyi - Shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Ezza ta arewa Peter Nweke, ya mutu, jaridar The Nation ta rahoto.

Nweke ya mutu ne sakamakon raunukan da ya ji bayan wasu da ake zaton yan daba siyasa ne sun farmake shi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris yayin zaben gwamnoni da na yan majalisar jihohi.

Shugaban PDP da aka kashe a Ebonyi
Yanzu Yanzu: Shugaban PDP Da Aka Yi Wa Mugun Duka a Ebonyi Ya Mutu Hoto: The Nation
Asali: UGC

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ta tabbatar da mutuwar Nweke a ranar Lahadi, 19 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Tsohon Kansila A Kano Har Lahira Kan Sace Akwatin Zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce an yi wa Nweke dukan tsiya sannan aka kwashe shi zuwa asibiti a cikin mawuyacin hali inda daga bisani likita ya sanar da mutuwarsa.

Onome ta ce rundunar yan sandan ta kaddamar da bincike a kan mutuwarsa da nufin kamawa da hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin.

Yadda abun ya faru

Kanin mamacin, Samson Nweke shima ya tabbatar da batun mutuwar tasa, rahoton Premium Times.

Ya bayyana cewa yan daba ne suka yi wa yayansa duka har sai da ya rasa inda kansa yake.

Kanin Nweke ya ce yan daban rike da bindigogin AK-47 sun farmaki rumfar zaben yayansa da ke PU 10, gudunmar Ogboji, karamar hukumar Ezza ta arewa, jihar Ebonyi.

A cewarsa, yan daban sun zo ne a kan babura biyu sannan suka kwamushe shi.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: "Za Mu Kashe Duk Wanda Ya Shirya Mutuwa a Yau" – Yan Sanda Sun Gargadi Masu Tada Zaune Tsaye

“Sun yi wa yayana, Mista Nweke Peter JP duka har bai san inda kansa yake ba.
“Yan daban sun kuma cinnawa kayan zabe wuta a rumfuna uku a Ndiagu Ogboji., rumfar 009, 010 da ta 011."

Kanin ya ci gaba da cewa:

“Makonni biyu da suka shige, Yaya Peter ya ziyarceni a Abakaliki. Bana gida amma ya hadu da matata. Ya fadawa matata da ta sanar da ni cewa nayi a hankali.
“Ya bayyana cewa wasu jam’iyyun siyasa sun lissafa wasu mutane daga garinmu da za a kashe kafin ko a ranar zabe. Ya ce shine na farko a jerin, ni ne na biyu da wasu mutum uku.
“A yau ya faru da mu. Yayin da na yi nasarar tsallake rijiya da baya, dan uwana bai samu dama ba. Sun kashe shi a rumfar zabena.
“Ina ma ace yau bai zo ba. Kaico! Ina ma ace ban taba sanin rana da ake kira 18 ga watan Maris din 2023 ba. Da dan uwa Peter bai mutu ba. Matashi mai jini a jika.”

Kara karanta wannan

Mota Dauke Da Yara Yan Makarantar Firamari Ta Yi Kundunbala A Legas

Yan sanda sun ceto jami'an INEC 19 da aka sace

A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar ceto wasu jami'an INEC 19 da aka yi garkuwa da su a jihar Imo a ranar zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng