Zan Zama Gwamna Idan Yan Uwana Mata Suka Zabe Ni, Aishatu Binani
- Aishatu Ahmed Binani ta ce idan yan uwanta mata suka ba ta haɗin kai cikin sauki zata lashe zaben jihar Adamawa
- Binani, Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, tana neman kwace mulki daga hannun gwamna mai ci na PDP
- Ta ce ta ji daɗin yadda maza ke ba ta goyon baya a zaben da aka san cewa mazan ne suka mamaye
Adamawa - Sanata Aishatu Binani, mai neman zama gwamna a inuwar APC a jihar Adamawa, ta ce ita zata samu nasara idan dukkan mata 'yan uwanta suka kaɗa mata kuri'a.
The Cable ta rahoto cewa Binani ta yi wannan furucin ne bayan ta jefa kuri'arta a rumfar 005, gundumar Bombai, ƙaramar hukumar Yola ta kudu.
"Wannan ba shi ne karo na farko da muka gudanar da zaɓe ba, ba da jimawa ba muka kammala zaben shugaban ƙasa da 'yan majalisun tarayya, kuma mun yi lafiya mun gama lafiya."
"Duniya ce ta maza amma na ji daɗi (yadda na shiga a fafata da ni a zaben da maza suka mamaye). Wannan karon mazan kansu suna goyon bayanmu yadda muka yi tsammani."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"A zamanin yanzu mata ke da mafi rinjayen kuri'u, idan baki ɗaya matan (jihar Adamawa) suka dangwala mun kuri'unsu, babu tantama mu zamu haye."
- Sanata Aishatu Binani.
Aishatu Binani, Sanata mai wakiltar mazaɓar Adamawa ta tsakiya a majalisar Dattawa, tana ɗaya daga cikin mata 11 da ke takarar zama gwamna a arewacin Najeriya.
Tana neman kwace mulki daga hannun gwamna mai ci, Ahmadu Umaru Fintiri, na jam'iyyar PDP, wanda ke neman tazarce zango na biyu a jihar Adamawa, arewa maso gabas.
Kawo yanzun dai a sakamakon da ke shigowa daga gundumomin Adamawa sun nuna cewa sai gwamna Fintiri ya yi dagaske kafin da iya zarcewa kan kujerarsa.
Jam'iyyar NNPP Ta Lashe Kujerar Ɗan Majalisar Dokoki
A wani labarin kuma jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta fara lashe kujerun 'yan majalisar dokokin jihar Kano
Baturen zabe a mazaɓar Rogo, ya ayyana Isma'il Falgore a matsayin zabbaben ɗan majalisar jiha mai wakiltar Rogo bayan samun kuri'u mafi rinjaye.
Asali: Legit.ng