Buhari ya Jefa Kuri’a, Ya Ba ‘Yan Najeriya Shawarar Zaben Karshe a Matsayin Shugaban Kasa

Buhari ya Jefa Kuri’a, Ya Ba ‘Yan Najeriya Shawarar Zaben Karshe a Matsayin Shugaban Kasa

Mai girma Muhammadu Buhari ya samu damar kada kuri’arsa a zaben Gwamnoni da Majalisa

  • Shugaban na Najeriya ya yi tir da ‘yan siyasar masu amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a
  • Buhari yace gwamnatinsa ta yaki siyasar kudi, ya fadawa al’umma da su zabi wanda suke so

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya fadawa masu yin zabe da su karbi kudi daga hannun ’yan siyasa idan har an nemi a saye ra’ayinsu.

The Cable ta rahoto Mai girma shugaban kasar yana cewa idan an ba mutane kudi su karba, amma dole su zabi ‘yan takaran da suke kauna.

Muhammadu Buhari ya yi wannan kira ne a ranar Asabar bayan ya kada kuri’arsa a zaben bana.

Kamar yadda ya saba yi, Shugaba Buhari ya yi zabe a akwati na 003 da ke mazabar Sarkin Yara A a karamar hukumar Daura a Katsina.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba na yiwa jama'a barazar ko su zabi APC ko su su dauki wani mataki a wata jiha

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari ya yi magana da 'yan jarida

Da yake magana da ‘yan jarida a cikin harshen Hausa da Ingilishi, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa tayi kokarin hana sayen kuri’u.

Buhari ya fadawa ‘yan siyasar da suke sayen kuri’un jama’a ko suke amfani da kudi domin lashe zabe da su daina wannan kazamar harka.

Buhari
Buhari yana zabe Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter
“Idan su (‘yan siyasa) sun ba ku kudi, ku karba, amma ku zabi ‘dan takaran da kuke so.”

- Muhammadu Buhari

Zaben shugaban kasa

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Buhari ya shaidawa manema labarai cewa ya ji dadin yadda mutane su ka zabi Bola Tinubu a Fubrairu.

A yau ne ake zaben Gwamnoni da wadanda za su zama ‘yan majalisar dokoki a jihohi.

Wannan karo, rahoton ya ce shugaban Najeriyan ya ki yarda ya bude takardar zabensa domin Duniya ta san wadanda ya kadawa kuri’a.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Ganduje Ya Fadawa Kanawa Su Zabi Abba Gida-Gida a Gobe

Yadda za a tattara sakamako

Kun ji labari idan an kammala kada kuri’a a rumfunan zabe, jami'in PO na INEC zai shigar da sakamakon zabe cikin takardar nan ta EC8A.

Za a dauki hoton EC8A da aka rattabawa hannu, a aika zuwa shafin duba sakamako. Ba hoton kurum za a tura ba, za a aika da takardun ga RAC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng