Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin INEC, Sun Lalata Kayan Zabe a Bayelsa
- Wasu mahara da ake zaton yan daban siyasa ne sun kwace kayayyakin zabe, sun ƙona su a karamar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun aikata wannan ɗanyen aiki ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare wayewar garin Asabar
- Gwamna Douyw Diri ya yi kira ga Sufeta da kwamishinan 'yan sandan jihar su dawo da zaman lafiya a yankin
Bayelsa - Wasu 'yan bindiga da ba'a sani ba kawo yanzu sun kai hari kuma sun ƙone kayyakin hukumar zaɓe INEC a cibiyar raba kayan zabe da ke garin Okodi, karamar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.
Tribune online ta tattaro cewa lamarin ya faru a awannin farko na wayewar garin Asabar, 18 ga watan Maris, 2023, ranar zaben yan majalisar jiha.
Wani ganau ya ce kayayyakin zabe na guduma ta 2, gunduma ta 4 da gunduma ta 5 a yankin Ogbia, Ogbia Constituency 2, sun ƙone ƙurmus a harin da misalin ƙarfe 3:00 na dare.
A cewar wani da abun ya faru a kan idonsa, harin ya kawo cikas a yunkurin mazauna yankin na zaben wanda ya kwanta masu a rai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an INEC da aka tura mazabar domin gudanar da zabe sun kam hanyar komawa Yenagoa, babban birnin Bayelsa domin tsira da rayuwarsu.
Sakataren watsa labarai na ofishin gwamnan Bayelsa, Mista, Daniel Alabrah, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar da sanyin safiyar Asabar.
"Wasu tsageru sun yi awon gaba da kayan zaɓen gundumomi masu lamba 2, 3, 4 da 5 da ke ƙarƙashin mazaɓa ta 2 a ƙaramar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa kuma sun lalata su."
"Gwamna Douye Diri ya yi Allah wadai da wannan ɗanyen aikin kuma ya roki Sufeta janar na rundunar 'yan sandaɓ kasar nan da kwamishinan 'yan sandan Bayelsa su dawo da zaman lafiya a yankin."
Shugaban sashin yaɗa labarai na INEC reshen Bayelsa, Wilfred Ifogah, wandaya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust, ya ce zasu fitarda sanarwa nan gaba kaɗan.
An yi wa PDP taron dangi a Neja
A wani labarin kuma LP Da NNPP Sun Cure Wuri Daya da APC Domin Ganin Bayan PDP a Neja
Jam'iyya mai kayan marmari da LP sun haɗa kai, sun ayyana goyon bayansu ga ɗan takarar gwamnan APC a jihar Neja, Umar Bago.
Asali: Legit.ng