Kai tsaye: Yadda Zaben Gwamna Yake Gudana a Jihohin Kaduna da Adamawa

Kai tsaye: Yadda Zaben Gwamna Yake Gudana a Jihohin Kaduna da Adamawa

Kaduna

A ranar 18 ga watan Maris 2023, mutanen Kaduna za su zabi wanda zai zama sabon Gwamna a cikin ‘yan takaran da suka tsaya zabe.

Kusan jam’iyyu ne a kan gaba wajen neman mulkin Kaduna, Uba Sani da Isa Ashiru Kudan.

Sauran ‘yan takaran su ne Jonathan Asake, Sulaiman Othman Hunkuyi, Muhammad Sani Sha’aban, da kuma Hayatu Lawal Makarfi.

Adamawa

A jihar Adamawa, a yau Aisha Dahiru Binani a Jam’iyyar APC za ta nemi ta kawo karshen Gwamnatin PDP ta Ahmadu Umaru Fintiri.

Nasarar Sanata Aisha Dahiru Binani yana nufin an samu mace ta farko a tarihin Najeriya da ta shiga zaben Gwamnan jiha, kuma tayi galaba.

Bayanai za su cigaba da zuwa daga Legit.ng Hausa yayin da abubuwa suke tafiya.

Abubuwa na tafiya dai-dai

Mutanen Kaura ta yamma a karamar hukumar Kaura da ke garin Kaduna su na yin zabe ba tare da an samu wata matsala ba.

A wani akwati da yake mazabar Jama'a a karamar hukumar Sabon Gari a Kaduna, wakilin jam'iyyar PDP ya kawo korafinsa.

PDP ta na zargin babu isassun takardun sakamakon zabe a akwati na 20 a Jama'a.

Matsalar BVAS

Situation Room sun rahoto cewa a wani akwati da yake Pakka a karamar Hukumar Maiha a Adamawa, na'rar BVAS ta samu tangarda.

Wannan jawo aka dakatar da tantace masu kada kuri'a, kuma an tsaida yin zabe.

A wani akwatin a yankin Mubi, babu wadanda ke layi domin kada kuri'a. An samu karancin wadanda suka fita yin zaben Gwamna a yau.

Ma'aikatan ICPC a U/Sarki

Jami’in Hukumar ICPC sun je rumfar da Gwamna Nasir El-Rufai yake kada kuri’arsa a Unguwar Sarki a Kaduna.

Punch ta ce an ga jami’an ne da karfe 9:35ns lokacin da mutane ke kokarin zabe.

Da karfe 11:42ns, hotunan Malam Nasir su ka fito a yayin da yake kokarin kada kuri'arsa a Ungwan Sarki.

Mai girma Gwamnan yana tare da Uwargidarsa, Hadiza Isma El-Rufai.

Binani tayi zabe

The Cable ta kawo rahoto cewa Aishatu Dahiru Binani ta kada kuri'arta a mazabar Bamboi a karamar hukumar Yola ta Kudu.

Sanata Aishatu Dahiru Binani ce ke neman takarar Gwamnan Adamawa a APC.

D/Trust ta rahoto 'yar takarar tana cewa ta hango alamun nasara, ta ce tana sa ran lashe zabe, ta kuma yabi yadda ake yin zaben.

Binani ta iso wurin zabe

Kimanin karfe 9:20ns, aka rahoto cewa Aisha Dahiru Binani ta hallara rumfarta domin tayi zabe a Yola.

Jama'a sun soma zabe

A wani akwati da ke layin Balarabe Musa a Narayi da ke karamar Chikun a jihar Kaduna, mutane sun fara zabe tun 8:00ns.

The Cable ta kawo wannan rahoto.

A wani akwati da yake Ungwan Yelwa a yankin na Chikun, mutane sun fara zabe kusan karge 9:00ns.

Rahoton Action Aid ya nuna BVAS ta na aiki lafiya lau, ba a samun wani rikici.

Ana raba kayan zabe a Kaduna

Hukumar INEC ta fara rabon kayan zabe zuwa rumfuna a Unguwar Mu'azu da ke jihar Kaduna.

Kayan zabe
Rabon kayan zabe Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Layin zabe a Girei

Abubuwa su na shirin kankama a Adamawa, BBC ta ce an hau layin zabe a garin Girei da ke jihar, mutane sun yi tanadi domin kada kuria'.

Shirye-shirye a Mubi

Bayanai sun nuna zuwa 8:00ns ma'aikatan zabe suka iso mazabar Lamorde a karamar hukumar Mubi ta Kudu a Adamawa.

Kafin nan an ga ma'aikatan zabe a rumfunan karamar hukumar Demsa.

Shirye-shirye a Yola

Bayanan da aka samu daga Hukumar INEC a Twitter sun nuna tun kafin karfe 8:00, ma'aikatan zabe sun isa karamar Hukumar Yola ta Arewa.

Ma'aikata sun hallara

Rahoto daga Situation Room ya nuna ma'aikatan zabe sun isa mazabar Nasarawa a karamar hukumar Yola ta Arewa tun 7:20ns.

Za a fara zabe a Yola

Zuwa karfe 7:21ns aka hangi malaman zabe a rumfar Makama a Yola da ke Adamawa.

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng