Farashin Man Fetur Zai Lula, Gwamnatin Tarayya Tana Shirin Barin Tinubu da Aiki
- Clement Agba ya yi karin haske kan inda aka kwana a kan batun janye tallafin man fetur a Najeriya
- Idan an cire tallafi farashin mai zai karu, saboda haka gwamnatin tarayya take yi wa ‘yan kasa tanadi
- Ministan tsare-tsaren kasa da kasafin Najeriya ya ce har yau kwamitin Osinbajo bai gama aikinsa ba
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu ba a tsaida magana a kan matakan da za a dauka idan an janye tallafin fetur a tsakiyar shekarar nan ba.
Daily Trust ta rahoto karamin Ministan tsare-tsaren kasa da kasafi, Clement Agba ya na bayanin nan bayan taron ‘Yan majalisar FEC a ranar Laraba.
Clement Agba ya amsa tambayoyi daga wajen manema labarai a fadar shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari ya jagoranci taron Ministocin.
Ministan ya nuna kwamitin da Farfesa Yemi Osinbajo yake jagoranta ya yi kusan shekara daya yana aiki, amma dai ba a kai ga cin ma matsaya ba.
Ana sauraron kwamitin Osinbajo
Agba ya shaidawa manema labarai su na sa ran kwamitin da yake aiki da Gwamnonin jihohi zai yanke shawara kan matsayar da za a dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Premium Times ta ce ba a ba kwamitin na Yemi Osinbajo wa’adi ba. Sai dai saura watanni biyu gwamnatin Muhammadu Buhari ta sauka daga mulki.
"Matakin da muke a yanzu shi ne na kokarin karkare magana a kan shawarwarin da aka samu daga bangarorin gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi.
Kun san cewa wannan wani lamari ne da zai shafi daukacin kasar nan. Dole a tabbata an tafi da kowa, ma’ana gwamnatin tarayya da matakin gwamnatocin jihohi.
- Clement Agba
Babu kudin tallafi bayan Mayu
Baya ga haka, Agba ya ce jam’iyyun PDP, APC da APGA, ‘yan kwadago, kungiyoyin matasa da mata, malaman addini da sarakuna duk su na da ta-cewa.
Daga jawabin Ministan, an fahimci gwamnatin tarayya tayi kasafin N3.3tr a matsayin kudin tallafin man fetur daga Junairu zuwa Yunin 2023.
An cire tallafin fetur a Ghana
Hakan na zuwa ne a lokacin da rahoto ya zo cewa gwamnatin Ghana ta janye tallafin fetur, aka bude asusu domin inganta matatun mai da ake da su.
Da zarar an dauki wannan mataki a Najeriya, ana sa ran farashin man fetur zai kara tsada. Yanzu haka ana kokawa da tsada da wahalar mai a kasar.
Ana wahalar samun fetur
Rahoto ya zo cewa a halin yanzu a Najeriya, maganar da ake yi, bayan dogayen layi, a wasu gidajen man, ana saida kowane litar man fetur a kan N400.
‘Yan bumburutu su na saida litansu a tsakanin N450 zuwa N500 saboda karancin fetur, ana tunani tun bayan zabe motoci suka daina dakon mai.
Asali: Legit.ng