Ebonyi: Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ya Janyewa Dan Uwan Umahi
- Wasu rahotanni dake yawo a jihar Ebonyi sun ce yar takarar mataimakin gwamna a inuwar APC ta yi murbus
- An ce Princess Obila ta hakura da takara a zaben ranar Asabar ne saboda matsalar rashin lafiya
- A wata sanarwa da sakataren APC ya fitar ya ce labarin ƙarya ce mara tushe da wasu masu neman suna suka kirkira
Ebonyi - Wasu rahotanni sun nuna cewa 'yar takarar mataimakin gwamnan APC a jihar Ebonyi, Patricia Obila, ta yi murabus, ta baiwa ƙanin gwamna Umahi tikitin takarar.
Vanguard ta ce labarin murabus ɗin Patricia Obila daga matsayin yar takarar mataimakin gwamna a inuwar APC na ci gaba da yawo a jihar Ebonyi, an ce ta sauka ne bisa dalilin rashin lafiya.
Masu ruwa da tsaki da jiga-jigan yan siyasa sun soki labarin murabus din Obila, wacce ta kama hanyar zama mataimakiyar gwamna mace ta farko a tarihin jihar idan APC ta lashe zaɓe.
Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta, ta ce labarin murabus din yar takarar ba wani abun mamaki bane domin gwamna Umahi zai iya aikata wa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta ce:
"Na ji labarin kuma ya jima da zama tsohon abu a jihar Ebonyi. Babu abinda ba zai yuwu ba a karkashin mulkin Umahi, ba abinda ba zai iya aikata wa ba,"
Shin menene gaskiyar labarin?
Da yake martani kan jita-jitar, Sakataren jam'iyyar APC a jihar Ebonyi, Charles Chukwuma Ofoke, ya ayyana labarin da ƙarya mara tushe balle makama.
A wata sanarwa da ya fitar, Mista Ofoke ya ce:
"Wannan kirkirarren labari ne da maƙiyan APC da gwamnatin Ebonyi karkashin mai girma gwmana Dave Umahi, suka ɓullo da shi. Sabanin ikirarin, Princess Obila lafiyarta kalau kuma ta shiryawa aiki."
"Makon da ya gabata sun yaɗa jita-jitar dan takarar gwamnan APC bai da lafiya, ba su ci nasara ba yanzu sun zo da wannan, duk Farfagandar su ba ta tsawon rai.
"Saboda haka muna kira ga ɗaukacin al'umma su yi watsi da labarin domin Farfaganda ce da masu neman suna suka kirkira."
PDP ta shiga ruɗani a jihar Kebbi
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Tsoffin Ministoci Biyu da Wasu Jiga-Jigai 5 a Kebbi
Jam'iyyar PDP ta tsinci kanta cikin yanayin ruɗani bayan ta dakatar da tsoffin Ministoci biyu da wasu jiga-jigai biyar.
Jim kaɗan bayan Sakataren PDP ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa, shugabn jam'iyya na jiha ya ce batun ba haka yake ba.
Asali: Legit.ng