“Wike Na Kashe Miliyan N50 Duk Sati Kan Barasa” - Amaechi

“Wike Na Kashe Miliyan N50 Duk Sati Kan Barasa” - Amaechi

  • Tsohon gwamnan Ribas, Chibuike Rotimi Amaechi ya bayyana Gwamna Nyesom Wike a matsayin mashayi
  • Amaechi ya ayyana hakan ne yayin da yake yi wa dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Ribas kamfen
  • Tsohon ministan ya kuma yi zargin cewa gwamnan na jihar Ribas na kashe kimanin miliyan N50 kan barasa duk sati

Rotimi Amaechi ya bayyana Gwamna Nyesom Wike a matsayin mashayi. Tsohon ministan sufurin kuma tsohon gwamnan ya yi zargin cewa Wike na kashe naira miliyan 50 a kan barasa duk mako.

Ya kara da cewar kada a bari gwamnan ya sake wa'adi na uku a fakaice, rahoton Thisday.

Gwamna Nyesom Wike da Rotimi Amaechi
“Wike Na Kashe Miliyan N50 Duk Sati Kan Barasa” - Amaechi Hoto: Rivers People
Asali: UGC

Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas, Tonye Cole, kamfen a karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamnan APC ya yi gargadin karshe, ya fadi abin da zai yiwa duk bankin ya ki tsoffin Naira

Tsohon ministan ya koka cewa yawan kudin jihar da Wike ke kashewa kan barasa a sati biyu, ya kusan yin daidai da kudin da shi (Amaechi) ya kashe wajen gina makarantar firamare daya lokacin da yake matsayin gwamna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka ya ce yana kawowa mutanen Ribas karan tsaye da kuma barnatar da kudin jihar.

Ya ce:

"Mutumin da Wike ke siyan barasa a wajensa, ya ce Wike na kashe naira miliyan 50 duk sati a kan barasa. Makarantun firamare da muka gina naira miliyan 112 ne, hakan na nufin a mako biyu Wike ke shanye makarantar firamare daya. Idan Wike ya yi magana, barasa ke magana. Kuma baya jin kunyar hakan. Wike ya fadama duniya baki daya a hirar kai tsaye cewa yana shan tsadadden barasa na shekaru 40, da safe.
"Muna kira ga INEC da ta zama a tsakiya. Mutane sun yi watsi da Wike da gwamnatinsa. Duk unguwar da na je, mutane na ta tsalle a kaina suna ihu. Suna tura cewa na gina gadajen sama biyar, ban yi rawa ba. Mun dauki sabbin likitoci 400, mun siya wa likitoci 600 motoci, mun siya motocin asibiti ga dukkanin asibitoci. Mun zagaya makarantun firamare don ganin abun da ke wakana, sannan mun gano babu malamai, don haka muka dauki malamai 13,200. A lokacin da na sauka daga mukamin Gwamna, akwai yan kwangila a kowace makaranta don kula da makarantar. Ina makarantun da shi (Wike) ya gina?"

A wani labari na daban, mun ji cewa jigon APC a Gombe, Jamilu Gwamna ya ce karya ne shi bai yi wa mutanen Gombe barazana da kisa ba kamar yadda wasu suka zarge shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng