Zaben Gwamnoni: Jerin Mata 24 Da Ke Neman Takara a Fadin Jihohin Najeriya
Za a gudanar da zaben gwamnoni a fadin jihohi 28 cikin 36 da ke Najeriya a ranar Asabar, 18 ga watan Maris. Akalla mata guda 24 ne za su fafata da takwarorinsu maza wajen neman kujerun gwamnoni a sassa daban-daban na kasar.
Legit.ng ta lura cewa yawan mata masu shiga harkar siyasa na kara karuwa a Najeriya musamman ma a zaben 2023.
Jam’iyyun siyasa 18 ne za su gabatar da yan takara a zaben amma mata biyu ne kawai suka lashe tikitin manyan jam’iyyun siyasa uku da suka hada APC mai mulki, babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma sabuwar jam’iyyar matasa ta Labour Party.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wacce ta fi shahara cikin yan takara 24 mata da ke neman kujerar gwamna a ranar Asabar ita ce Aishatu Dahiru Binani, wacce ke rike da tutar APC a jihar Adamawa.
Ga cikakkun jerin mata 24 da ke neman kujerar gwamna a zaben
- Aishatu Dahiru Binani – APC a jihar Adamawa
- Gladys Johnson-Ogbuneke - SDP a jihar Abia
- Lancaster Okoro – PRP a jihar Abia
- Ekanem Abasiekeme - AA a jihar Akwa Ibom
- Udoh Emem Monday - SDP. a jihar Akwa Ibom
- Roseline Chenge - ADP a jihar Benue
- Aondona Dabo-Adzuana - ZLP a jihar Benue
- Abubakar Fatima - ADP a jihar Borno
- Ibiang Marikana Stanley - ADP a Cross River
- Onokiti Helen Agboola - Accord a jihar Delta
- Cosmas Annabel – APP a jihar Delta
- Chinenye Igwe - APM a jihar Ebonyi
- Ogochukwu Nweze - SDP a jihar Enugu
- Umar Binta Yahaya - AA a jihar Jigawa
- Yakubu Furera Ahmad - BP a jihar Kano
- Mahmud Aisha – NRM a jihar Kano
- Motunrayo Jaiyeola – APM a jihar Kwara
- Funmilayo Kupoliyi - APM a jihar Lagas
- Roseline Adeyemi - APP a jihar Lagas
- Patricia Tsakpa - ADP a jihar Nasarawa
- Khadijah Abdullahi-Iya - APGA a jihar Neja
- Aduragbemi Euba - YPP a jihar Oyo
- Beatrice Itubo - LP a jihar Rivers
- Hadiza Usman - ZLP a jihar Zamfara.
Jerin jihohi 15 da PDP ka iya lashewa a zaben gwamnoni na 2023
A wani labarin kuma, mun kawo cewa hasashe sun nuna cewa jam'iyyar PDP mai adawa a kasar ka iya nasara wajen kaso kujeru 15 a zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar.
Asali: Legit.ng