Zaben Gwamnoni: Jerin Jihohin Da PDP Ka Iya Lallasa APC Da Sauran Jam’iyyu a Cikinta
A ranar 18 ga watan Maris ne yan Najeriya a jihohi mabanbanta za su fita rumfunar zabe domin zabar yan takarar da za su jagorance su a matsayin gwamnoni na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Za a gudanar da zabukan gwamnonin ne a fadin jihohi 28 daga cikin 36 na Najeriya.
A wannan zauren. Legit.ng Hausa ta jeranto maku wasu jihohi da ake ganin babbar jam'iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP) zata iya lashewa a zabukan gwamnonin masu zuwa.
Kamar yadda hasashen kungiyoyin Enough is Enough (EiE) da SB Morgen (SBM) suka nuna, jam'iyyar PDP na iya lashe jihohi 15 a zabe mai zuwa.
Ga rin jihohin da ake ganin PDP za ta iya yin nasara a zabukan gwamnonin
- Sokoto
- Kebbi
- Oyo
- Katsina
- Kaduna
- Bauchi
- Gombe
- Adamawa
- Cross River
- Akwa Ibom
- Rivers
- Delta
- Taraba
- Ebonyi
- Plateau
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zabukan gwamnoni sun fi na shugaban kasa rikitarwa, NSA Monguno
A wani labari na daban, babban mai ba kasa shawara a kan lamarin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno, ya bayyana cewa zabukan gwamnoni da za a yi a ranar 18 ga watan Maris, zai fi na shugaban kasa da aka yi rikitarwa.
Sai dai kuma, Monguno wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, 15 ga watan Maris, ya ce basa hango kowani rikici ko hargitsi da ke kawo kai ko zai tarwatsa tsarin a yan kwanaki masu zuwa.
Duk da haka, ya ce shugaban ma'aikatan tsaro da sufeto janar na yan sanda wadanda sune kan gaba a tsarin tsaron zaben suna ta ganawa don tabbatar da an yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yakubu Dogara ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan APC a Bauchi
A wani lamarin kuma, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya ayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bauchi, Air Marshal Sadiqque Baba Abubakar mai ritaya gabannin zabe.
Dogara ya bayyana cewa dan takarar PDP a zaben kuma gwamna mai ci, Bala Mohammed bai yi wani abun a zo a gani a jihar ba don haka ya bukaci al'ummar jihar da su tsige shi a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng