Zaben Gwamnoni Ya Fi Na Shugaban Kasa Matsala – NSA Monguno

Zaben Gwamnoni Ya Fi Na Shugaban Kasa Matsala – NSA Monguno

  • NSA Babagana Monguno ya ce hukumomin tsaro za su yi aiki ba ji ba gani don tabbatar da an yi zaben gwamnoni cikin lumana
  • Mai ba kasar shawara kan tsaro ya bayyana cewa zabukan gwamnoni sun fi na shugaban kasa rikitarwa
  • Sai dai ya ce hukumomin tsaro basu hango wani rikici da ke tunkaro kasar ba a yan kwanaki masu zuwa

Abuja - Mai ba kasa shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, ya bayyana cewa zaben gwamnoni da na yan majalisun jihohi ya fi matsala.

Sai dai kuma, Monguno ya ce hukumomin tsaro basa hango barkewar rikici ko kawo tsaiko ga tsarin zaben, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Monguno ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 14 ga watan Maris a Abuja a wajen taron kwamitin tuntuba kan tsaron zabe na ICCES.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: An Tsinci Gawar Farfesan Wata Fitacciyar Jami'a Ɗauke da Wasu Abubuwa a Jikinsa

Mai ba kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Monguno
Zaben Gwamnoni Ya Fi Na Shugaban Kasa Matsala – NSA Monguno Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A cewarsa, ana ta gudanar da taro daban-daban musamman da shugaban ma'aikatan tsaro da sufeto janar na yan sanda.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Monguno ya ce:

"Zabukan ranar Asabar za su fi rikitarwa, kuma za su dan sha banban. Abu na farko, za mu samu mazabu 1,021 wanda hakan ke nufin za a samu karin mutane masu sha'awar zaben, kuma za a samu karin mutane da za su kada kuri'a. Shakka babu abubuwa za su sha bamban da zabukan da aka kammala.
"Ga hukumomin tsaro, na san anyi abubuwa da dama. ina ta tattaunawa da shugaban ma'aikatan tsaro, da IGP, wadanda sune shugabannin hukumar da ke kan gaba a tsarin zabe. Zuwa yanzu, bama hasashen komai da zai zama mai muni ko matsala ba a yan kwanaki masu zuwa. Amma hakan ba yana nufin cewa duk mu yi watsi da shirinmu ba. Ya zama dole mu bi tsari. Ya zama dole mu ba kowa damar sauke hakkinsu a matsayinsu na yan kasar nan."

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Jam'iyyu 5 Sun Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

Ya kuma bukaci jam'iyyun siyasa da yan takara da su nuna da'a da dattako lokaci da bayan zabe, musamman ta hanyar saita magoya bayansu, rahoton Punch.

Shugaban INEC ya ja hankalin jam'iyyun siyasa

Da yake jawabi, shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci jam'iyyun siyasa da su gargadi magoya bayansu.

Yakubu ya kuma bukaci IGP da ya kula da dukkan laifukan zabe domin hukumar na sa ran karbar takardun karar.

Jam'iyyu 4 na shirin maja a jihar Nasarawa don daddake APC daga mulki

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu fitattun jam'iyyun siyasa hudu suna shirin yin maja a kokarinsu na tsige dan takarar APC kuma gwamna mai ci, Abdullahi Sule daga kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng