"Jam'iyyar APC Bata Cancanci Sake Mulkin Jihar Borno Ba", Dan Takarar NNPP

"Jam'iyyar APC Bata Cancanci Sake Mulkin Jihar Borno Ba", Dan Takarar NNPP

  • Ɗan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen gwamnan jihar Borno ya caccaki gwamnan jihar, Babagana Zulum
  • Dr Umar Alkali ya bayyana cewa gwamnan ko kaɗan Zulum bai cancanci sake komawa kan kujerar sa ba
  • Ɗan takarar ya kuma zargi jam'iyyar APC a jihar da tafka maguɗin zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata

Jihar Borno- Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Borno, Dr Umar Alkali, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, bai cancanci ya koma kan kujerar sa ba.

Ɗan takarar ya bayyana gwamnan a matsayin fankan ba kilishi domin babu wani abin a zo a gani da ya taɓuka a jihar.

NNPP Borno
"Jam'iyyar APC Bata Cancanci Sake Mulkin Jihar Borno Ba", Dan Takarar NNPP Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Dr Umar Alkali ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise Tv ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Jam'iyyu 5 Sun Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce

"Mutane a waje suna kallon Zulum a matsayin ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa aiki, amma mu mutanen jihar Borno, muna kallon sa a matsayin gwamnan da yafi kowa rashin taɓuka abin kirki a tarihin jihar mu." Inji shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu ƴan jihar ne mun san dukkanin abinda ke gudana a jihar, babu wani abu ɗaya tilo na cigaba a jihar, ba wai batun kawai gina gadoji bane."
"Mutanen jihar Borno suna rayuwa ne cikin ƙangin talauci, ba su buƙatar gadar sama, satin da ya wuce na je sansanin ƴan gudun hijira a Bama, an ajiye mutane a wajen kamar dabbobi, ba tsaftataccen ruwa ba asibiti ba makaranta a wajen."

Ɗan takarar ya bayyana cewa idan aka zaɓe su, za su mayar da hankali kacokan wajen yin ayyukan da zasu amfani rayuwar al'umma.

Ya Zargi APC da yin maguɗin zaɓe a jihar

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Fusata, Ya Shirya Tona Asirin Tsaffin Ɓarayin Gwamnonin Jihar Kaduna

Da yake tsokaci kan zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata, Dr Alkali Usman, ya zargi jam'iyyar APC da yin ƙarfa-ƙarfa wajen murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihar.

Yace gwamnatin jihar tayi amfani da ƙarfin mulki wajen ganin ta tauye sakamakon zaɓen jihar, inda yace jam'iyyar su ta NNPP ta samu ƙuri'u sosai a jihar.

2023: Jam'iyyu 5 Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Gwamnan Jihar Yobe

A wani labarin na daban, jam'iyyu biyar a jihar Yobe sun koma bayan gwamnan jihar, a zaɓen ranar Asabar.

Gwamna Mai Mala Buni yana neman sake komawa mulki a karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng