'Yan Takarar Gwamna 7 Sun Janye, Sun Koma Bayan Gwamnan Jihar Legas

'Yan Takarar Gwamna 7 Sun Janye, Sun Koma Bayan Gwamnan Jihar Legas

  • Ƴan takarar gwamna bakwai sun haƙura da takara ana saura kwana huɗu a fafata a zaɓen gwamnoni
  • Ƴan takarar sun haƙura da takara inda suka koma bayan gwamnan APC na jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu
  • Sun yi kira ga magoya bayan su da tabbatar sun sake zaɓen gwamnan a karo na biyu domin cigaba da ayyukan da yake kwararawa a jihar

Jihar Legas- Ƴan takarar gwamna bakwai da jam'iyyu tara sun marawa gwamnna jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, baya yayi tazarce.

Wannan goyon bayan na zuwa ne daga gamayyar jam'iyyu masu rajista (ARPP), wanda aka sanar a ranar Litinin a Legas. Rahoton Punch

Sanwo
'Yan Takarar Gwamna 7 Sun Janye, Sun Koma Bayan Gwamnan Jihar Legas Hoto: Punch
Asali: UGC

Jam'iyyun taran sune, All Peoples Party; Action Democratic Party; Allied Peoples Movement; National Rescue Movement; Young Progressives Party; New Nigeria Peoples Party; Zenith Labour Party; Social Democratic Party da People’s Redemption Party.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Takarar Gwamna 6 Sun Janye Daga Takara Kwana 5 Gabanin Zabe

Sun bayyana cewa sun yanke wannan hukuncin ne saboda ayyukan da Sanwo-Olu ya kwarara a jihar wanda ya sanya suka ga cancantar sa da ya cigaba mulki a karo na biyu. Rahoton Thisday

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mun yanke wannan hukuncin ne bayan dogon nazari kan dukkanin ayyukan kawo cigaba a Legas. Ba zamu iya yin fatali da nasarorin da wannan gwamnatin ta samu ba kawai saboda bambancin ra'ayin siyasa."
"Nasarorin da gwamna yake ta samu abin a yaba ne wanda ya cancanci ace an cigaba da su."

Sun yi nuni da cewa yana da kyau ace jihar ta kasance a hannun ɗan jam'iyyar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu domin amfana yadda yakamata.

“A irin wannan lokacin jihar Legas zai fi kyautuwa ace tana a hannun jajirtattu kuma ƙwararrun shugabanni. Zaɓen Sanwo-Olu tabbas goyon baya ne ga cigaba da jihar Legas." Inji su

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Tsageru Sun Kaiwa Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Mummunan Hari a Kaduna, Sun Tafka Ɓarna

Jam'iyyun sun kuma buƙaci magoya bayan su da su sake zaɓen Sanwo-Olu da mataimakin sa Obafemi Hamzat, a ranar Asabar.

Ƴan takara 7 da suka janyewa Sanwo-Olu sun haɗa da, Ajayi Adebayo (YPP), Mrs Adeyemi Abiola (APP), Adenipebi Mode Adekunle (ZLP),  Kupoluyi Funmi (APM), Braithwate Akinwynmi (NRM), Olanrewaju Kamal (NNPP), da Ishola Bamidele (ADP).

Mukarrabin Jonathan Ya Fadi Yaudarar da Tinubu ya yi Amfani da Ita Wajen Doke Atiku

A wani labarin na daban kuma, wani na kusa da Jonathan ya bayyana hanyar da Tinubu ya bi ya doke Atiku a zaɓen shugaban ƙasa.

Atiku Abubakar bai kai labari ba a zaɓen shugaban ƙasa inda yayi rashin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng