'Yan Takarar Gwamna 6 Sun Janye, Sun Koma Bayan Gwamnan Adamawa
- Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ƙara samun goyon baya bayan wasu yan takara na jam'iyyu 6 sun kai masa ziyara
- Yan takarar gwamna har su 6 sun amince zasu mara baya ga kudirin Fintiri na neman tazarce a zaben gwamna mai zuwa
- Fintiri na jam'iyyar PDP na fuskantar barazana mai girma daga Sanata Aishatu Binani, yar takarar gwamna a inuwar APC
Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintire, ya samu gagarumin ƙarin goyon baya a kudirinsa na neman tazarce a zaben gwamna mai zuwa ranar Asabar.
Gwamnan ya samu ƙarin karfi ne bayan wasu 'yan takarar gwamna 6 na jam'iyyun adawa a Adamawa sun amince za su mara masa baya domin tabbatar da ya samu nasara.
PM news ta tattaro cewa 'yan takarar gwamnan guda 6 sun ayyana cikakken goyon bayansu ga gwamna Fintiri a Yola, babban birnin jihar Adamawa ranar Litinin.
Bugu da ƙari, sun umarci baki ɗaya magoya bayansu da mambobin jam'iyyun su, su zabi Ahmadu Fintuiri, wanda ke neman tazarce a inuwar jam'iyyar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen yan takarar da suka janye
Yan takarar da suka yanke shawarin janyewa bayan sun zauna da Fintiri sun haɗa da, Malam Bello Babajo na jam'iyyar APM, Malam Yahaya Chulde na APGA, da Emmanuel John-Yerima na NRM.
Sauran su ne, Ambrose Zenith na Zenith Labour Party (ZLP) da kuma Babangida Furo na Action Democratic Party (ADC).
A madadinsu baki ɗaya, Mista Babajo, ya ce sun cimma matsayar mara wa gwamna mai ci baya ne bayan neman shawari daga masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam'iyyunsu.
Ya ce gwamnatin Fintiri ta baiwa mara ɗa kunya musamman a bangaren ayyukan raya ƙasa, walwalar ma'aikata da kuma tsaro.
"Mun tsaida shawarin mara wa gwamnati mai ci baya saboda nasarorin da ta samu kuma zamu yi aiki don tabbatar da Fintiri ya zarce kan kujerar gwamna," inji shi.
A wani labarin kuma Abokin Takarar Atiku Ya Fasa Kwai, Ya Faɗi Manyan Dalilin da Yasa Peter Obi Ya Samu Nasara a Shiyyoyi 2
Gwamnan Delta, Ifeayi Okowa, ya ce Peter Obi ya samu nasara a kudu ne saboda wasu abubuwa da suka mamaye zuƙatan mazauna shiyyoyi biyu.
Ya ce taken Obidient, Addini na cikin abubuwan da suka baiwa tsohon gwamnan Anambra nasara a yankin.
Asali: Legit.ng